Wasu jam’iyyu sun nemi mu sayar masu katunan zabe – INEC
Kwamishinan Zabe na Jihar Oyo, Barista Mutiu Agboke ya ce, yanzu haka wasu jam’iyyu da ’yan siyasa a jihar sun fara neman alfarma daga Hukumar INEC a jihar don ta sayar musu da katunan zabe ta yadda zasu yi amfani da su wajen magudi a zabe mai zuwa. Kwamishinan Zaben ya fadi haka ne a […]
Kwamishinan Zabe na Jihar Oyo, Barista Mutiu Agboke ya ce, yanzu haka wasu jam’iyyu da ’yan siyasa a jihar sun fara neman alfarma daga Hukumar INEC a jihar don ta sayar musu da katunan zabe ta yadda zasu yi amfani da su wajen magudi a zabe mai zuwa.
Kwamishinan Zaben ya fadi haka ne a jawabinsa wajen taron kara wa juna ilmi da Kungiyar ’Yan jarida Masu Watsa Rahotanni ta Intanet (OMPAN) ta shirya a Ibadan. Ya ce, hukumar ta yi wa mutum miliyan 2 da dubu 900 rajista a jihar, inda yanzu haka akwai katunan zabe dubu 914 da 529 da ba a karba daga hannunta ba.
Barista Agboke wanda bai fadi sunayen jam’iyyu da ’yan siyasar da suka nemi hukumar ta sayar musu da katunan zaben ba, ya ce, “Wadannan mutane suna neman abin da babu kuma suna da masaniyar babu abin da suke bukata. Ku shaida wa masu neman sayan katunan zabe su saya a wani wuri domin ba za su samu ko daya a Jihar Oyo ba. Ina tabbatar muku cewa babu jami’in Hukumar INEC da zai sayar da katin zabe ga kowane dan siyasa. Kuma ina kara tabbatar muku cewa za a gudanar da zabe lami lafiya a Jihar Oyo.”
Kwamishinan ya nemi ’yan jarida a jihar su bayar da hadin kai da goyon baya ga hukumar wajen watsa dukan muhimman labarai ga jama’a “Domin dukanmu mu ne masu ruwa-da-tsaki a kan wannan al’amari.
Saboda haka ya kamata mu duka mu yi aiki tare domin tabbatar da an gudanar da zabe lami lafiya a Jihar Oyo,” inji shi.
Ya nuna rashin jin dadi game da kin yin rajista da al’ummar Jihar Oyo suka fito da ita inda ya yi kiran su hanzarta canja wannan hali domin amfanin kansu.