Wasu Kananan hukumomi sun fara fita kangin Coronavirus a Katsina

Sakamakon bullar cutar coronavirus da aka samu a Jihar Katsina wadda tayi sanadiyyar rufe wasu kananan hukumomi tara daga cikin 34 da ke Jihar, a yanzu wasu daga cikinsu sun fita daga kangin cutar. A wata sanarwar da ta fito daga ofishin Sakataren gwamnatin Jihar Dokta Mustafa Inuwa ya sanyawa hannu ta ce, kananan hukumomin […]

Wasu Kananan hukumomi sun fara fita kangin Coronavirus a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari

Sakamakon bullar cutar coronavirus da aka samu a Jihar Katsina wadda tayi sanadiyyar rufe wasu kananan hukumomi tara daga cikin 34 da ke Jihar, a yanzu wasu daga cikinsu sun fita daga kangin cutar.

A wata sanarwar da ta fito daga ofishin Sakataren gwamnatin Jihar Dokta Mustafa Inuwa ya sanyawa hannu ta ce, kananan hukumomin Mani da Safana sune suka fara fita daga samun bullar wannan cuta a cikinsu.

Hakan yasa Gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin janye dokar zaman gida da aka sanya kananan hukumomin daga ranar Juma’ar data gabata.

A ranar Asabar aka kara samun karin karamar hukumar Jibiya wadda ita ma aka tabbatar da cutar a cikinta wadda ta zamo ta uku daga cikin tara da aka rufe.

Kamar yadda Gwamna Masari ya ambata a wata hira da DW Hausa suka yi da shi ya ce, “Nan gaba kadan za a bude sauran wuraren da aka rufe domin bayar da damar yin shirye-shiryen bukukuwan sallah wanda zai hada har da sallar idi.”