Wasu karin mutum biyar sun kamu da coronavirus a Kano
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce an samu karin mutum biyar da suka kamu da cutar coronavirus a jihar. Da safiyar Laraba ne Kwamishinan Lafiya na jihar Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya sanar da a shafin Twitter na Ma’aikatar Lafiya ta jihar, @KNSMOH. COVID-19: An killace mutum biyu a asibitin Kafanchan COVID-19: An killace […]
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta ce an samu karin mutum biyar da suka kamu da cutar coronavirus a jihar.
Da safiyar Laraba ne Kwamishinan Lafiya na jihar Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya sanar da a shafin Twitter na Ma’aikatar Lafiya ta jihar, @KNSMOH.
- COVID-19: An killace mutum biyu a asibitin Kafanchan
- COVID-19: An killace mutum biyu a asibitin Kafanchan
Sanarwar ta ce zuwa karfe 10:25 na safiyar Laraba, adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus a Kano ya kai tara.
Wednesday, 15th April 2020. As at 10:25 am, 5 additional cases of #COVID19 have been confirmed in @KanostateNg @NCDCgov @FMICNigeria @dawisu @NOA_Nigeria @Chikwe_I @NphcdaNG
#StaySafeNigeria #StayHome pic.twitter.com/8KfIOT2Bih— Kano State Ministry of Health (@KNSMOH) April 15, 2020
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka sanar da mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar ta Kano, lamarin da ya sa ta shiga cikin jihohin da ke da masu dauke da ita.
Tuni dai gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita ta mako guda daga ranar Alhamis.