Wasu ma’aikatan Jihar Oyo sun samu kyautar Naira miliyan 15
Wasu ma’aikatan gwamnatin Jihar Oyo, sun samu garabasar kyautar Naira miliyan 15 da dubu dari 6, wadda Gwamna Abiola Ajimobi ya rarraba ga wadanda suka yi nasara, a dalilin kwazonsu ga aiki. Gwamnan ya raba kyauta ce a ranar Litinin a wajen wani taron addu’ar fara aiki a cikin sabuwar shekara ta 2014. Addu’ar, wadda […]
????????????????????????????????????

Wasu ma’aikatan gwamnatin Jihar Oyo, sun samu garabasar kyautar Naira miliyan 15 da dubu dari 6, wadda Gwamna Abiola Ajimobi ya rarraba ga wadanda suka yi nasara, a dalilin kwazonsu ga aiki.
Gwamnan ya raba kyauta ce a ranar Litinin a wajen wani taron addu’ar fara aiki a cikin sabuwar shekara ta 2014. Addu’ar, wadda aka gudanar a kusa da ofishin gwamna da ke Sakatariyar gwamnati a Agodi Ibadan, ta samu halartar kusoshin gwamnati da manya da kananan ma’aikata.
Cikin jawabinsa, Gwamna Ajimobi ya ce ma’aikatan sun cancanci samun wannan garabasa, musamman a dalilin kwazonsu ga ayyukan da aka damka musu.
Gwamnan, wanda ya ambaci kyautar Naira miliyan 10 ga dukkan ma’aikatan da suka halarci wajen addu’ar, ya bayar da kyautar Naira miliyan 5 ga dukkan ma’aikatan hukumar samar da ruwan sha ta jihar, a dalilin namijin kokarin da suka yi wajen cika alkawarin kammala ayyukan kwaskwarima da aka yi wa madatsar ruwa ta Asejire, wacce ta shafe shekaru 17 ba ta aiki.
Har ila yau, wata ma’aikaciya a sashen dab’i, Uwargida Margret Olatoun Oluwafemi ta samu kyautar Naira dubu 250, tare da sauran ma’aikatan wannan sashen, wadanda su ma kowanensu ya samu kamar haka wato Naira dubu250, duk a dalilin buga ingattattun takardun da aka yi amfani da su a wajen addu’ar. Shi kuwa Mista Oyelola Okunola na ofishin Safiyo-janar, ya samu kyautar Naira dubu 100 ne saboda kyawawan sutura da yake sanye da su da ya burge mahalarta taron addu’ar.
Gwamnan, wanda ya ce duk wadannan kyautuka sun fito ne daga cikin aljihunsa (ba aljihun gwamnati ba), kuma ya nemi dukkan ma’aikatan gwamnati su jajirce wajen nuna hazaka da kwarewa domin tabbatar da ganin sun sauke nauyin da ke kansu.