Wasu mahara sun kashe mutum 20 a Zamfara

Kimanin mutum 20 ne suka riga mu gidan gaskiya  sakamakon auka masu da wasu suka yi cikin dare, babu zato babu tsammani.Malam Lawalli Mashema, ya shaida yadda al’amarin ya faru, kasancewar a kan idanunsa abin ya faru. Ya ce cikin tsakiyar dare ne, mutanen kauyen Mashema da ke gundumar Kekun Waje, a karamar Hukumar Maru […]

Wasu mahara sun kashe mutum 20 a Zamfara
Wasu mahara sun kashe mutum 20 a Zamfara

Kimanin mutum 20 ne suka riga mu gidan gaskiya  sakamakon auka masu da wasu suka yi cikin dare, babu zato babu tsammani.
Malam Lawalli Mashema, ya shaida yadda al’amarin ya faru, kasancewar a kan idanunsa abin ya faru. Ya ce cikin tsakiyar dare ne, mutanen kauyen Mashema da ke gundumar Kekun Waje, a karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara suna cikin barci sai suka ji hayaniya ta yi yawa. Ya ce shi da dan uwansa mai suna Adamu nan take suka tashi, sai daga bisani suka fahimci babu lafiya, don haka suka nemi wurin buya.
Ya ce daga bisani bayan sun fahimci wasu mutane ne suka shigo gari dauke da makamai kuma suna da matukar yawa, sun fi 100. Sun samu nasarar kashe kusan mutum 20, a yayin da suka raunata wasu da yawa, wadanda a halin da ake ciki yanzu suna asibiti. Malam Lawalli ya kara da cewa, maharan sun kore masu dabbobi masu yawa, wadanda suka hada da shanu da awaki.
Abdul Malik Zubairu, dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Bungudu da Maru, ya bayyana bakin cikinsa da faruwar wannan al’amarin. Ya ce wadanda suka riga mu gidan gaskiya an yi masu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
DSP Sanusi Amiru, shi ne jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar wannan al’amari kuma ya bayyana cewa bayan sun samu labarin faruwarsa, sun tura jami’ansu amma har yanzu ba su samu nasarar kama kowa ba. Jihar Zamafara dai ta jima tana fama da irin wadannan hare-haren wanda har yanzu an kasa shawo kansu. Hakan ya hana mazauna kauyuka samun kwanciyar hankali.