Wasu mahara sun kona motar safa a Saudiyya
Rahotanni daga kasar Saudiyya ya ce wasu mutane dauke da makamai sun banka wa wata motar-safa wuta, wadda ke dauke da ma’aikata za ta kai su wuraren aiki a lardin gabashin kasar.Kafafen yada labaran kasar dai sun ce babu wanda ya jikkata, haka kuma ba a san wanda ya kai harin ba tukuna.Kodayake, an kai […]
Rahotanni daga kasar Saudiyya ya ce wasu mutane dauke da makamai sun banka wa wata motar-safa wuta, wadda ke dauke da ma’aikata za ta kai su wuraren aiki a lardin gabashin kasar.
Kafafen yada labaran kasar dai sun ce babu wanda ya jikkata, haka kuma ba a san wanda ya kai harin ba tukuna.
Kodayake, an kai harin ne a lokacin da ake zaman dar-dar a yankin, bayan hukuncin kisan da aka zartar wa wani fitattcen Malamin Shi’a, Nimr al-Nimr, wanda aka zarga da aikata ta’addanci.
Malamin dai ya yi rayuwarsa ne a lardin gabashin kasar, inda yake wa’azi, kuma lardin wuri ne da mabiya akidar Shi’a suka yi kaka-gida, wadanda kuma ke jin cewa mabiya akidar Sunni da ke da rinjaye kasar na mayar da su saniyar-ware.