Wasu malamai da fastoci sun yi wa ’yan siyasa gwanjon addini – Solomon Dalung

Barista Solomon Dalung na daya daga cikin wadanda suka suka halarci taron kara wa juna sani na kungiyar Debelopment Initiatibe of West Africa a Minna a matsayin daya daga cikin hanyoyin kara samar da fahimta a tsakanin mabiya manyan addinan kasar nan Musulmi da Kirista inda ya gabatar da kasida a taron. Wakilinmu ya nemi […]

Wasu malamai da fastoci sun yi wa ’yan siyasa gwanjon addini – Solomon Dalung
Wasu malamai da fastoci sun yi wa ’yan siyasa gwanjon addini – Solomon Dalung

Barista Solomon Dalung na daya daga cikin wadanda suka suka halarci taron kara wa juna sani na kungiyar Debelopment Initiatibe of West Africa a Minna a matsayin daya daga cikin hanyoyin kara samar da fahimta a tsakanin mabiya manyan addinan kasar nan Musulmi da Kirista inda ya gabatar da kasida a taron. Wakilinmu ya nemi karin haske game da wasu al’amuran da ya tabo a kasidarsa:

Aminiya: Me za ka ce game da wannan taro na fahimtar juna a tsakanin mabiya addini da aka shirya a nan Minna?

Barista Dalung: Tarurruka irin wadannan suna da matukar muhimmanci kwarai da gaske wurin wanzar da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki a kowace al’umma, musamman irin tamu mai dimbin al’adu da addinai. Wannan taron, ya zo a daidai lokacin da aka gama zabubbuka a Najeriya, don haka yana da fa’ida, saboda idan ka yi la’akari da yanayin yadda siyasa da addini suke gudana, irin wadannan tarurruka kan kawo sauki, tare da kawo fahimta kan wasu kura-kuran da aka tafka yayin da ake neman mulki. Zama tare dai dole ne, ko mun ki ko mun so, ko mun yarda ko ba mu yarda ba. Wasu daga cikinmu Musulmi ne, wasu daga Kiristoci, wasu ma ba su da addini, kuma dukkanmu ’yan Najeriya ne.
Aminiya: Wadanne al’amura ne aka tabo a taron da suka burge ka?
Barista Dalung: Babban abin da ya burge ni a taron shi ne, an fito kiri-kiri an gaya wa juna gaskiya, abubuwan da suke sosa wa Kirista rai sun fito sun fada, haka ma Musulmi suka yi. Ka ga ba a yi wa juna rufa-rufa ba. Babbar matsalar da ’yan Najeriya suke fama da ita, ita ce ta rufa-rufa.Yau idan Musulmi ya ce ma kafiri ba ka ji dai ba, sai ka tambaye shi, wa kake nufi? Sai ya ce, kai nake nufi. Idan kuma Musulmi ya aikata laifi, sai Kirista sai su ce Musulmi sun zauna sun shirya ne. An dauka cewa Musulmi ne suka shirya al’amarin Boko Haram. Wannan bai kamata ba, wannan ne ya sa aka shafa wa Musulmi kashin kajin da ya yi tasiri marar kyau. Idan aka yi la’akari da wasu halaye da Kiristoci ke aikatawa wadanda ba su kamata ba, an aike su aikata haka ne?
Aminiya: Yayin da kake gabatar da kasida, ka nuna cewa Musulmi sun fi Kiristoci fuskantar kalubale, me kake nufi?
Barista Dalung: Idan ka dauki tarihin addinan Musulunci da na Kirista, ai Annabi Isah (AS) ya zo shekaru da dama kafin Annabi Muhammad (SAW), ke nan an yi shekaru da yawa ana yada addinin Kiristanci kafin addinin Musulunci. Da aka fara addinin Musulunci, yayin da matsafa suka taso wa Musulmi, ai Kiristoci ne suka shiga gaba suka ce wadannan ’yan uwanmu ne. Da haka suka karbe su suka ba su mafaka, to ina aka ajiye wannan dangantakar da aka samo tun farko? Wannan ya sa Musulmi cikin babban kalubale, domin duk abin da da Musulmi daya ya aikata, sai a yi wa abin fassara cewa an zauna ne aka tsara lamarin. In ma an zo a fadi ga abin da shugaba ya aikata sai a ce tunda yake shugaba ne ga shi. Ana misali da maganar hana gina mujami’u a Arewa, ana dauka cewa Musulmi ne suka ce kada a bayar da filayen gini, ba haka ba ne. Son zuciyar mutumin da aka zaba ne ya kai shi ga aikata haka, tunda lokacin da yake neman a zabe shi, bai nuna zai aikata haka ba.
Aminiya: Me za ka iya fadi game da malaman Musulunci da na Kirista da suke yada koyarwar da ta saba wa littattafansu?
Barista Dalung: Wadannan sun sa ’yan uwansu a cikin tsaka mai wuya. Muna da malamai da fastoci nagari wadanda har yau suna tsaye ne kan alkiblar da addinansu suka tanada a littattafansu. Babban abin takaici shi ne, akasarinsu sun yi wa ’yan siyasa gwanjon addinan nan, su kuwa ’yan siyasa suka saye, kuma suna wa’azi a masallatai da majami’unsu kamar da gaske. Ka ga ke nan, an gurbata addini da siyasa, siyasa kuma neman mulki ne, neman mulki kuma kamar neman zuma ne. Mutum kuma ya zubar da zuma haka kawai, ba karamin aiki ba ne. Muna bukatar malaman da suka riki akida ta kwarai bisa koyarwar littattafansu su ci gaba da haka, don su dawo kan hanya. Ga wadanda suka kama hanyar daji kuwa abin da nake son su fahimta shi ne, in ma ana yi ne don siyasa ne, zaben bana ya nuna cewa talakawa sun kwato kayansu. Dimokuradiyya kayansu ne, duk wanda suke so shi za su zaba.
Aminiya: Wadanne darussa biyu ne da zabubbukan bana ke tare da su?
Barista Dalung: Babban darasi shi ne, idan kai mutumin kirki ne, wanda halayenka suka bayyana ga jama’a, babu ko shakka jama’a za su yi maka sakamako, muddin ka fito neman abu a nan duniya ba sai an je Lahira ba. Abu na biyu wanda na koya shi ne talaka a Najeriya yana da tasiri. Ba abin da ba a yi ba, kudi bai bayar da mulki ba, in dai za ka yi amfani da kudi ne a zabubbuka kuma, ba zai sake tasiri ba. Duk wadanda aka zaba a bana, ba za su tare a Abuja ba dole su koma wurin jama’arsu, muddin suka ki zama tare da jama’arsu, sun san cewa kuri’a na hannun talakawa, muddin suka kyalla ido ba su gansu ba, sun san sauran.
Aminiya: Wane kira za ka yi wa ’yan Najeriya?
Barista Dalung: ’Yan Najeriya mu kaunaci juna da zuciya daya. Allah ne Ya hallice mu, kuma Ya hada mu a kasa daya. Babu yadda za mu samu ci gaba muddin ba mu zauna lafiya ba. ’Ya’yanmu su yi biyayya ga iyayensu da magabata, yin haka zai sa mu kasance cikin kasar da za mu yi alfahari da ita, kuma ta zama abin koyi ta kowace fuska.