Wasu masu katin wucin-gadi za su yi zaben gwamnoni —Kotu ga INEC

Kotu ta ce babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya ko Dokar Zabe suka ce masu katin zabe na dindindin kadai ne za su kada kuri’a

Wasu masu katin wucin-gadi za su yi zaben gwamnoni —Kotu ga INEC

Kotu ta umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bar wasu masu katin zabe na wucin gadi su kada kuri’a a zaben gwamnoni da majalisun dokokin jiha da ke tafe ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ba da umarnin ne bayan wasu ’yan Najeriya biyu, masu suna Kofoworola Olusegun da kuma Wilson Allwell, sun shigar da karar neman INEC ta bari masu katin zabe na wucin-gadi su yi zaben da ke tafe.

Ya ce “Kotu na umartar INEC ta bar masu karar su yi amfani da katin zabe na wucin-gadi da ta ba su, tunda dai ta yi musu rajista kuma bayanansu na cikin rajistar zabe.

“Masu kara na da ’yancin amfani da katin zabensu na wucin-gadi a zabe mai zuwa tunda sun riga sun yi abin da ya rataya a kansu na rajistar zabe kuma bayanansu sun fito a rumbun adana bayanai da sauran takardun zabe da INEC ta wallafa,” in ji alkalin.

Sai dai ya bayyana cewa izinin amfani da katin zabe na wucin-gadi ya kebanci Kofoworola Olusegun da Wilson Allwell ne kawai, banda sauran masu zabe, kasancewar masu karar ba su shigar da ita a matsayin na wakilci ba.

“Tunda ba a matsayin wakilci aka kawo karar ba, ba ni da hurumin amsa bukata ta uku, ta barin duk halastattun masu katin zabe na wucin-gadi su kada kuri’a,” in ji alkalin.

Amma ya bayyana cewa babu inda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ko Dokar Zabe suka ce masu katin zabe na dindindin kadai ne za su kada kuri’a.

Ya ce hatta sashe na 47 na dokar zabe, katin zabe kawai ya yi magana, bai ce sai na dindindin ba.

Da yake magana kan hukuncin, lauyan masu kara, Victor Opatola, ya bayyana hukuncin kotun a matsayin nasara ga ’yan Najeriya da suka sha wahalar yin rajisar zabe, amma ba su samu katinsu na dindindin saboda kurewar lokacin, kuma ba laifinsu ba ne.

A cewarsa tun da har wadanda yake wakilta sun yi duk abin da doka ta ce na yin rajista, amma har lokacin ba da katin dindindin ya wuce ba su samu nasu ba, to ya kamata a bari su yi zabe.

Opatola, ya ce abin da ya kamata bisa adalci, shi ne a bar sauran ’yan Najeriya suka cika sharudda kamar wadanda yake wakilta suka cika, su  yi zabe, domin bayanan da ke katin zabe na wucin-gadi su ne ke kan katin dindindin.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa a halin da ake ciki, wajibi ne bin umarnin kotun ga INEC, har sai idan kotun daukaka kara ta jingine hukuncin.

Kawo yanzu INEC ba ta ce komai ba a kan hukuncin, amma ta sha nanata cewa masu katin zabe na dindindin kadai ne za su jefa kuri’a a zabukan 2023.