Wasu masu tabin hankali sun haifi jarirai a kasuwa
Wasu mata biyu masu tabin hankali sun haifi jarirai a kasuwanni da ke Legas da Ibadan. daya daga cikinsu mai suna Esther, mai kimanin shekaru 25, ta haifi jaririnta ne a bainar jama’a a kan titin Adisa Akintoye da ke kusa da kasuwar Ketu a Legas, yayin da dayar mai suna Sadiat Oladiti, mai shekaru […]

Wasu mata biyu masu tabin hankali sun haifi jarirai a kasuwanni da ke Legas da Ibadan. daya daga cikinsu mai suna Esther, mai kimanin shekaru 25, ta haifi jaririnta ne a bainar jama’a a kan titin Adisa Akintoye da ke kusa da kasuwar Ketu a Legas, yayin da dayar mai suna Sadiat Oladiti, mai shekaru 30, ta haifi tagwaye a unguwar Orita Challenge a Ibadan.
Wani direba mai suna Solomon Ayinde da al’amarin ya auku a kan idanunsa a Legas, ya shaida wa Aminiya cewa, wasu mata da ke hada-hadar kasuwanci ne suka lura da halin da Esther ke ciki, suka hanzarta kai mata dauki ta hanyar yin amfani da zannuwansu suka zagaye ta. Bayan ta haihun ne suka garzaya da ita zuwa wani asibitin haihuwa da ke kusa, inda aka ci gaba da kula da ita. Mata sun yi ta kai gudunmawar suturun yara da sauran abubuwan bukatu ga Esther.
Solomon ya bayyana cewa wata kungiya mai zaman kanta tana shirin mayar da Esther zuwa ainihin mahaifarta da ke Jihar Ondo.
Shi ma Oba na Ketu, wanda ya jagoranci wasu fadawansa zuwa asibitin, ya bayar da gudunmawar da ba a bayyana ba kuma ya umarci hukumar kula da jin dadin mata da kananan yara ta yankin Ketu ta dauki alhakin dawainiyar matar da jaririnta.
Ita kuwa Sadiat Oladiti, wadda haifaffiyar garin Ibadan ce, ta fara nakuda ne a bainar jama’a a unguwar Orita Challenge, amma sai mazauna unguwar suka garzaya da ita zuwa cibiyar kiwon lafiya ta rundunar ’yan sanda, inda ta samu kulawa har ta haifi tagwayen nata.
Matar Shugaban karamar Hukumar Oluyole, Uwargida Oluwatoyin Aleshinloye da mukarrabanta sun ziyarci asibitin tare da bayar da gudunmawar kudi da kayan bukatun jarirai, mijinta Yarima Ayodeji Abass Aleshinloye kuma ya umarci karamar hukumar ta tabbatar da ganin an yi wa matar da tagwayenta kyakkyawar kulawa.
Uwargida Oluwatoyin ta mika godiyarta ga babban jami’in ’yan sanda (DPO) na Orita Challenge saboda irin gudunmawar da ya bayar.
Dangin Sadiat da suka ziyarci ssibitin, sun ki yarda su yi wani bayani ga ’yan jarida, sai dai sun gode wa Uwargida Oluwatoyin kan abin da ta yi domin kula da mai jegon.