Wasu matasa sun guntule wa juna hannu a Yobe
’Yan sanda sun cakfe wasu matasa biyu da suka sare wa junansu hannanye a Jihar Yobe. Matasan sun guntule wa junansu wuyan hannu ne a lokacin da suke fada da juna a garin Alkali da ke Karamar Hukumar Dapchi ta jihar. An harbe wani tsohon babban sojan sama da jikansa a Kaduna Jarirai 4 sun […]
’Yan sanda sun cakfe wasu matasa biyu da suka sare wa junansu hannanye a Jihar Yobe.
Matasan sun guntule wa junansu wuyan hannu ne a lokacin da suke fada da juna a garin Alkali da ke Karamar Hukumar Dapchi ta jihar.
- An harbe wani tsohon babban sojan sama da jikansa a Kaduna
- Jarirai 4 sun rasu a gobarar asibiti a Indiya
A wata sanarwa da mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Yobe, ASP Dungus Abdulkarim, ta ce matasan biyu “Sun yi kazamin fada ne da adduna, wanda ya kai ga kowannensu ya yanke wa junansu wuyan hannu.
“Ba a kai ga gano musabbabin fadan ba, domin dukkansu suna kwance rai kwakwai, mutu kwakwai a Babban Asibitin Tarayya da ke Nguru ana jinyar su.”
A cewarsa, wadanda ake zargin masu shekara 25 ne, kuma ana kyautata zaton ’yan daba ne.
Ya ce ana kan gudanar da bincike a kan lamarin kuma an dauki tsauraran matakai domin yin maganin masu aikata laifuka a jihar.