Wasu matasan Jos sun goyi bayan Jang kan tsayawa takarar Sanata

Wasu gungun matasa da ke garin Jos fadar Jihar Filato sun shirya gangamin nuna goyan baya ga tsayawar Gwamnan Jihar Mista Jonah Jang takarar SanatanMazabar Filato ta Arewa a karkashin Jam’iyyar PDP a ranar Litinin da ta gabata. Da yake jawabi a wajen taron wani mai taimaka wa Gwamna Jang, Mista Gary Pam ya ce […]

Wasu matasan Jos sun goyi bayan Jang kan tsayawa takarar Sanata
Wasu matasan Jos sun goyi bayan Jang kan tsayawa takarar Sanata

Wasu gungun matasa da ke garin Jos fadar Jihar Filato sun shirya gangamin nuna goyan baya ga tsayawar Gwamnan Jihar Mista Jonah Jang takarar SanatanMazabar Filato ta Arewa a karkashin Jam’iyyar PDP a ranar Litinin da ta gabata.

Da yake jawabi a wajen taron wani mai taimaka wa Gwamna Jang, Mista Gary Pam ya ce a cikin dukkan wadanda suke takarar Gwamnan Jihar Filato da Sanatan Filato ta Arewa babu wadanda suka yi abubuwan kyautata wa rayuwar al’ummar jihar kamar Gwamna Jonah Jang da Sanata GNS Pwajok da ke takarar Gwamna a karkashin PDP.
Mista Gary Pam ya ce babu shakka idan aka zabi wadannan mutane za su yi iyakar kokarinsu wajen bunkasa garin Jos da Jihar Filato baki daya.
Ya ce babu abin da zai kawo zaman lafiya da ci gaba a jihar sai hadin kai, don haka ya yi kira ga al’ummar jihar su hada kai su zauna lafiya da junansu.
A jawabin shugaban matasan da suka shirya taron, Malam Izzul Arab danlami ya ce sun shirya taro ne domin su nuna goyon bayansu ga Gwamna Jonah Jang kan ya tafi Majalisar Dattawa da kuma dan takarar Gwamnan Jihar karkashin PDP, Sanata GNS Pwajok domin su ci gaba da irin kyawawan ayyukan da suke yi a jihar.
Ya ce gwamnatin Jang ta taba zuciyar matasa a jihar ta hanyar raba musu motoci sama da 100 ba tare da nuna bambanci ba. Har ila yau ya ce Gwamna Jang ya yi ayyuka da dama na kyautata rayuwar al’umma kamar hanyoyin mota a kowane bangare na jihar. Ya ce, “Babu shakka mun shaida cewa Gwamna Jang yana tafiya da al’ummar Jos, domin a farkon mulkinsa ya ba dan Jos Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar tare da ba wani dan Jos Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar kuma ya raba wa al’ummar Musulmin jihar kujerun aikin Hajji. Don haka ya yi kira ga al’ummar Jos su fito su zabi Gwamna Jang a matsayin Sanatan Filato ta Arewa da Sanata GNS Pwajok a matsayin Gwamnan Jihar.