Wasu muhimman bukukuwan aure da suka dauki hankali a 2014

A shekarar da ta gabata, an samu daure-dauren aure da dama. Wadansu sun zo sun wuce ba tare ma da jama’a sun sani ba, wasu kuwa sun dauki hankalin mutane ta fuskoki da dama.Wasu daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin jama’a a wasu bukukuwan auren sun hada da salo-salo daban-daban na kek da aka […]

Wasu muhimman bukukuwan aure da suka dauki hankali a 2014
Wasu muhimman bukukuwan aure da suka dauki hankali a 2014

A shekarar da ta gabata, an samu daure-dauren aure da dama. Wadansu sun zo sun wuce ba tare ma da jama’a sun sani ba, wasu kuwa sun dauki hankalin mutane ta fuskoki da dama.
Wasu daga cikin abubuwan da suka dauki hankalin jama’a a wasu bukukuwan auren sun hada da salo-salo daban-daban na kek da aka rika gabatarwa a bukukuwan. Irin wadannan kek sun hada da wanda Tosan ya zayyana a Legas da wanda aka gabatar a Fatakwal, wanda aka yi wa lakabi da ‘Kek din Alfarma.’ Akwai kuma kek iri daban-daban da aka gabatar a bukukuwan da suka faru a Abuja.
Bikin auren Maryam da Jibrin Abdulmumini ya gudana ne a biranen Abuja da Birnin Kebbi kuma biki ne da ya kayatar matuka. An daura auren ne dai a Birnin Kebbi, sannan aka yi kamun amarya, aka sanya ta lalle duk dai a can.
A dandalin shakatawa na Harrow Park da ke Abuja, nan aka gabatar da kwarya-kwaryan shagalin cin abincin dare. Nan ne dai makada da mawakan zamani suka rakashe. Mawaka irin su Omawunmi da Timi Dakolo, duk suna daga cikin wadanda suka baje kolin fasaharsu a bukukuwan.
A bikin auren Faith Sakwe kuwa, an kayatar da ’yan bikin, inda aka gabatar da wani dogon kek mai daukar hankali, wanda aka yi wa zayyana da kalolin tutar Najeriya. An daura auren ne a ranar 5 ga Afirilu a Bayelsa, a yayin da kuma aka gabatar da kasurgumin shagali a ranar 12 ga wannan wata, a Abuja. Ita dai Faith, diya ce ga Shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Akwai kuma bikin auren A’isha dangiwa da Mustapha da ya gudana a shekarar da ta gabata. Shi ma wannan biki ya dauki hankalin mutane matuka. An daura auren nasu ne a watan Maris. Amaryar ta gwangwaje da suturu masu kayatarwa, wadanda aka yi wa zayyana tamkar na dawisu. An ce a Dubai aka yi dinkin kayan.
Bikin auren Abba Atiku Abubakar da amaryarsa Mariana Saleeby belile, shi ma ya kayatar kuma ya dauki hankali sosai.

A-Kurkura: Guba ko Magani?

Tsohon Shugaban Jami’ar Ilori, Farfesa Ambali ya rasu

ICPC ta hana El-Rufai ganin likita —Hadiminsa

Hanyoyin zuwa Katsina sun zama tarkon mutuwa