Wasu samari biyu sun yi wa budurwa fyade
Ana zargin wadansu matasa biyu makiyaya da shekarunsu ba su kai 20 ba masu suna Lawal Abdullahi da Shaini kan yi wa wata budurwa (an sakaya sunanta) mai kimanin shekara 15 fyade bayan da suka tare ta a kan hanyarta ta komawa gida daga aiken da mahaifiyarta ta yi mata zuwa wurin ’yar uwarta a […]
Ana zargin wadansu matasa biyu makiyaya da shekarunsu ba su kai 20 ba masu suna Lawal Abdullahi da Shaini kan yi wa wata budurwa (an sakaya sunanta) mai kimanin shekara 15 fyade bayan da suka tare ta a kan hanyarta ta komawa gida daga aiken da mahaifiyarta ta yi mata zuwa wurin ’yar uwarta a ranar Alhamis ta makon jiya a Unguwar Albishir a karamar Hukumar Chanchaga ta Jihar Neja.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa a lokacin da budurwar ta yi tozali da matasan da suka bi ta, ta nemi dan acaban da ya dauke ta ya bi da ita wata hanya domin kauce musu, don kai aiken ga mahaifiyarta.
Majiyar ta ce bayan budurwar ta sallami dan acabar tana hanyar karasawa gidansu, sai matasan suka tare ta suka kwace Naira dubu 10 da za ta kai wa mahaifiyarta, sannan suka kamata da kokawa da suka ci karfinta sai suka yi mata fyade.
Majiyar ta ce budurwar tana zuwa gida ta shaida wa mahaifiyarta abin da ya faru, nan take mahaifiyar ta garzaya wurin Sarkin Fulanin yankin, ta sanar da shi.
Sarkin Fulanin Alhaji Muhammad Tukur Abubakar, bai bata lokaci ba wurin gabatar da karar matasan a hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, inda jami’an rundunar suka je unguwar suka yi awon gaba da su.
Majiyar ta ce babu wata alaka da ta taba hada samarin da budurwar a baya. Kuma ta yi mamaki kan yadda aka bar yaran suke cin karensu babu babbaka a yankin. “Dalili, sun dade suna yi wa mutane fashi musamman da maraice ga wadanda ke kan hanyarsu ta komawa kauyukansu bayan sun gama cin kasuwa, ga satar dabbobin da suke yi ga mazauna yankin baki daya,” inji majiyar.
Aminiya ta gano cewa iyayen yaran ne suke daure wa musu gindi a duk lokacin da suka aikata laifi, ta amfani da kudi domin ganin an sako yaran a duk lokacin da aka kama su.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Neja ASP Oguche Richard Adamu ya ce, lamarin bai isa ofishinsa ba.