Wasu sun jahilce ni, ni ba na bogi ba ne- Buhari

A jiya Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi ba na bogi ba ne, ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da al’ummar Najeriya mazauna kasar Poland a birnin Krakow a ziyarar da ya kai kasar domin halartar taron sauyin yanayi na Majalisar dinkin duniya. A yayin ganawar, wani dan Najeriya ne […]

Wasu sun jahilce ni, ni ba na bogi ba ne- Buhari

A jiya Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa shi ba na bogi ba ne, ya bayyana hakan ne a ganawar da ya yi da al’ummar Najeriya mazauna kasar Poland a birnin Krakow a ziyarar da ya kai kasar domin halartar taron sauyin yanayi na Majalisar dinkin duniya.

A yayin ganawar, wani dan Najeriya ne ya yi masa tambaya a kan cewa shin da gaske ne cewa shi ne Buhari da aka sani ko kuma wani ne ke kwaikwaiyon sa da ake kira Jibril daga Sudan.

Shugaban ya yi Allah wadai masu yada wannan jita-jitar tare da cewa, ba su san ya kamata ba, kuma abu ne da ya saba wa koyarwar duk wani addinin kasar.