Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa
Ministan ya gargaɗi gwamnoni kan yin sulhu da ‘yan bindiga, inda ya ce maharan na amfani da hakan wajen sake sabon shiri.
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa ci gaba da matsalar ta’addanci da fashi da makami a ƙasar na faruwa ne saboda goyon bayan da ’yan ta’adda ke samu daga wasu ɗaiɗaikun mutane da ke ba su abinci, bayanan sirri da kuma kuɗaɗen shiga.
Ya bayyana haka ne wajen jawabin da ya gabatar a wajen babban taron ƙasa da aka gudanar a Jihar Legas.
- Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Abuja kan matsalar tsaro
- Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga
Ministan ya jaddada cewa akwai mutanen da ake haɗa baki da su da kuma waɗanda ke ɗaukar nauyin ’yan ta’addan a cikin al’umma, waɗanda ya ce su ne ke ci gaba da rura wutar ta’addanci a Najeriya.
Ministan ya bayyana cewa jami’an tsaro na fuskantar ƙalubale wajen kai hare-hare saboda ’yan bindigar na fakewa a cikin fararen hula.
Janar Musa ya ƙara da cewa duk wanda aka kama yana taimaka wa ’yan ta’adda ko yin kasuwanci da su, za a ɗauke shi a matsayin ɗan ta’adda.
Ya buƙaci al’umma da su gaggauta fallasa masu haddasa rikici da masu tallafa musu domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabi ƙasar, musamman Arewacin Najeriya.
Tsohon Janar ɗin sojin ya gargaɗi gwamnonin jihohi da su daina yin sulhu da ’yan ta’adda, yana mai cewa hakan ba mafita ba ce, face dabarar da ’yan bindigar ke amfani da ita wajen sake shirya kansu.