Wasu ‘yan majalisa sun sake fita daga APC

Wasu karin ‘yan majalisar Wakilan Tarayya biyu na jam’iyyar APC sun sake sanar da aniyarsu na fita daga jam’iyyar. A zaman Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya da aka yi yau Alhamis, Kakakin Majalisar Yakubu Dogara ne ya karanta wasikar fita daga jam’iyyar APC. ‘Yan majalisar biyun su ne Ahmed Abu daga jihar Neja da Stephen Olemija […]

Wasu ‘yan majalisa sun sake fita daga APC

Wasu karin ‘yan majalisar Wakilan Tarayya biyu na jam’iyyar APC sun sake sanar da aniyarsu na fita daga jam’iyyar.

A zaman Majalisar Wakilan Tarayyar Najeriya da aka yi yau Alhamis, Kakakin Majalisar Yakubu Dogara ne ya karanta wasikar fita daga jam’iyyar APC. ‘Yan majalisar biyun su ne Ahmed Abu daga jihar Neja da Stephen Olemija daga jihar Ondo. Ahmed Abu ya koma jam’iyyar SDP yayin da Stephen Olemija ya koma AA.

Duk ‘yan majalisar biyu sun bayyana rashin amincewar su da zaben fidda gwani na APC da aka gudanar a jihohin su.

 

Cikakken rahoton na nan tafe.