Wasu ’yan siyasa na kokarin shirya wa gwamnatin Tinubu mummunar zanga-zanga – DSS
DSS ta ce ta gano mutanen kuma tana sanya musu ido
Hukumar tsaro ta DSS ta ce ta gano shirin da wasu ’yan siyasa ke yi na shirya wa Shugaban Kasa Bola Tinubu mummunar zanga-zanga.
DSS, wacce ba ta bayyana sunan mutanen ba, ta ce suna kokarin yin amfani da kungiyoyin dalibai da na kabilu da na matasa wajen cim ma burin nasu.
- Tinubu zai tattauna da ’yan kwadago kan shirinsu na fita zanga-zanga
- Magidantan da ’yan bindiga suka kashe a masallaci a Kaduna sun bar marayu 61
A cewar hukumar, ana son shirya zanga-zangar ce domin a nuna gazawar Gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro a kan abin da suka bayyana da manufofin tattalin arziki.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Kakakin hukumar, Peter Afunanya ya fitar a ranar Litinin.
Sanarwar ta ce tana ankarar da jama’a ne bisa bayanan sirrin da ta samu.
Sai dai ta ce tuni ta gano masu kokarin kitsa zanga-zangar, kuma tana nan tana zuba musu ido.
Daga nan sai DSS ta yi kira ga manyan makarantu da su ja kunnen dalibansa da kada su kuskura a yi amfani da su wajen yi wa zaman lafiyar kasa zagon kasa.