Wasu ’yan ta’adda sun shiga hannu a Jihar Katsina

Rundunar ’Yan sanda a Jihar Katsina ta gabatar wa manema labarai wani da ake zargi da yin fashi da makami tare da satar shanu mai suna Ibrahim Umar, wanda ake yi wa lakabi da Oro, da shekara 25 da ke kauyen ’Yankuzo na karamar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara. Oro, wanda ya fada komar jami’an tsaron […]

Wasu ’yan ta’adda sun shiga hannu a Jihar Katsina

Rundunar ’Yan sanda a Jihar Katsina ta gabatar wa manema labarai wani da ake zargi da yin fashi da makami tare da satar shanu mai suna Ibrahim Umar, wanda ake yi wa lakabi da Oro, da shekara 25 da ke kauyen ’Yankuzo na karamar Hukumar Tsafe, Jihar Zamfara.

Oro, wanda ya fada komar jami’an tsaron shi da kansa ya amsa cewa yana daga cikin kungiyar mutum 15 da suke fashi da makami tare da satar shanu a tsakanin jihohin Katsina da Zamfara. Ya nuna a fili irin yadda ya iya sarrafa bindiga ciki kuwa har da kwancewa tare da daure ta.

Kazalika, ya shaida cewa ya shiga cikin kai hare-hare sama da 30 walau na fashi da makami ko satar shanu a tsakanin wadannan jihohi biyu. Ya ce a iya saninsa, ya kashe mutane hudu kawai.

Yayin da aka tambaye shi ko ta yaya ya samu bindigar da yake amfani da ita da kuma inda bindigar take a halin yanzu, Oro ya ce ya saye ta kuma a halin yanzu tana can ya boye har sai lokacin da aka nemi ya kawo, tun da an yi sulhu da su kusan shekara guda da ta wuce.

“Ni ban ga laifin da na yi ba da aka kawo ni nan, in kuma akwai a kawo shi. Iyaka gwamnati ta nemi bindigarta in ba ta a kyale ni in koma gida wajen iyalina, tun da ina da mata,” inji shi.

Oro wanda har zuwa lokacin da manema labarai ke yi masa tambayoyi bai nuna wata alama ta nadamar abin da ya yi ba, hasali ma tambayar laifin da ya yi da aka tsare shi yake yi.

Kazalika, rundunar ta gabatar da wasu da ake zargin yin fashin a gidan wani mutum da ake kira Umar Lawal na Unguwar Baro da ke cikin karamar Hukumar Malumfashi, wadanda suka hada da Muhammad Tukur Isa da Muhammad Muddaha Isa, dukkansu da ke garin Unguwar Alhaji Lawal, karamar Hukumar Kafur.