Wasu yara uku sun guje wa mahaifinsu saboda musgunawa

Masarautar Zuba da ke yankin Birnin Tarayya Abuja, tana ci gaba da kula da wasu yara uku a fadarta wadanda aka same su a babbar tashar motar garin sama da wata daya da ya wuce.  Sarkin Fadar Zuba, Malam Muhammad Murtala ya shaida wa Aminiya cewa, yaran uku masu suna Fatima Auwal mai shekara 11 […]

Wasu yara uku sun guje wa mahaifinsu saboda musgunawa
Wasu yara uku sun guje wa mahaifinsu saboda musgunawa

Masarautar Zuba da ke yankin Birnin Tarayya Abuja, tana ci gaba da kula da wasu yara uku a fadarta wadanda aka same su a babbar tashar motar garin sama da wata daya da ya wuce. 

Sarkin Fadar Zuba, Malam Muhammad Murtala ya shaida wa Aminiya cewa, yaran uku masu suna Fatima Auwal mai shekara 11 da kanwarta A’isha Auwal, mai shekara 7 da karaminsu Kabiru Auwal mai shekara 5, an same su ne suna watangaririya a tashar, inda suka ce sun baro gidansu ne da ke garin Jiwa a Abuja da suke zaune da mahaifinsu da matarsa.
Da take amsa tambayar wakilinmu, babbarsu Fatima Auwal ta ce ta dauko kannenta ne da nufin zuwa wurin mahafiyarsu da ke kauyen Kasanga a karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja, inda ta yi zargin cewa matar mahaifinsu tana musguna musu kuma duk lokacin da suka sanar da mahaifinsu sai ya yi musu duka. Ta ce mahaifinsu yana umartar matarsa ta hana su abinci a duk lokacin da suka ce ya kai su wurin mahaifiyarsu.
Madakin Zuba Malam Umar Ahmad wanda Sarkin Zuba Alhaji Muhammad Bello Umar ya damka masa alhakin kula da yaran, ya ce duk kokari da suka yi don gano gidan yaran ko mahaifinsu, bai samu nasara ba.
Da aka tuntubi Babban Jami’in ’Yan sandan Zuba, Muhammad Mahmud Umar, ya ce ba a sanar da ofishinsu faruwar al’amarin ba.