Wata ɓaraka ta kunno kai a Kwankwasiyya
A kwanakin baya ne dai wata ƙungiya ta ɓullo a fagen siyasar Kano mai suna ‘Abba Tsaya da Ƙafarka.
Babbar ɓaraka ta kunno kai a tafiyar siyasar Kwankwasiyya ta Jam’iyyar NNPP, inda ’yan majalisar tarayya biyu a jihar suka sanar da ficewa daga tafiyar.
Mataimakin shugaban marasa rinjaye a Majalisar Wakilai, Alhaji Ali Sani Madakin Gini ya tabbatar da cewa, ya fita daga tsagin Kwankwasiyya a cikin Jam’iyyarsa ta NNPP.
Ɗan majalisar mai wakiltar Dala a tsakiyar birnin Kano ya tabbatar da haka ne, bayan wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, wanda a ciki aka ji yana cewa, “daga yau, na daina harkar Kwankwasiyya”.
A cikin bidiyon, Alhjai Ali Madakin Gini ya bayyana cewa, “Kwankwasiyya ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce”.
Ya ƙara tabbatar da cewa, “na fahimci cewa, an gina tafiyar Kwankwasiyya ce kawai domin ci gaban Kwankwaso”.
Haka shi ma takwaransa da ke wakiltar ƙananan hukumomin Kibiya da Rano da kuma Bunkure, Alhaji Kabiru Alhassan Rurum ya sanar da raba gari da tafiyar ta Kwankwasiyya.
A cewar Alhaji Alhassan Rurum ya fice daga tafiyar ce sakamakon ‘rashin adalci’ daga ɓangaren uban tafiyar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Zuwa yanzu dai ba a ji wani martani daga ɓangaren Sanata Kwankwaso ba a kan wannan iƙirari.
Duka ’yan majalisar biyu, sun bayyana cewa, har yanzu suna nan a Jam’iyyarsu ta NNPP, amma ba tsagin jagorancin Sanata Rabi’u Kwankwaso ba.
Matakin na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Kano, wanda Jam’iyyar NNPP ta lashe dukkan kujerun.
’Yan majalisun biyu, wato Alhaji Ali Madakin Gini da Alhaji Kabiru Alhassan Rurum sun yaba wa Gwamnan Kano Injiniya Abba
Kabir Yusuf da cewa, shi mutumin kirki ne don haka sun shawarce shi da ya yi duk yadda zai yi, ya ‘tsaya da ƙafarsa’.
A kwanakin baya ne dai wata ƙungiya ta ɓullo a fagen siyasar Kano mai suna ‘Abba Tsaya da Ƙafarka’ mai rajin gwamnan na Kano ya daina biyayya ga jagoran Kwankwasiyya, ya ci gashin kansa lamarin da ya janyo Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da wani kwamishina, bisa zargin su da alaƙa da ƙungiyar.