Wata 1 bayan harin Tudun Biri

Abin da ya faru cikin wata guda tun bayan da jirgin soji ya kai wa masu taron Mauludi a kauyen Tudun Biri

Wata 1 bayan harin Tudun Biri

A rana irin  ta yau, 3 ga Disamba, 2023, wani jirgin soja mara matuki ya yi wa mutanen da ke halartar taron Mauludi ludugen bom har sau biyu a kauyen Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Akalla mutane 100 ne suka rasu a wannan mummunan hari, cikinsu har da mutum 34 ’yan gida daya, da wasu mutun shida ’ya’yan mutum daya, da dai sauransu, bacin wadanda suka samu munanan raunuka.

Girman barnar harin

Wadanda suka tsallake rijiya da baya a harin sun ce ana cikin taron Mauludin da misalin karfe 9 na dare suka ji shawagin jirgin soji, inda kafin su ankara, sai dai suka ji fashewar bom din da jirgin ya sako musu.

Ana cikin aikin ceto wadanda harin ya ritsa da su, kimanin mintoci 30 bayan harin farko, sai jirgin ya dawo ya kara jefa wa masu aikin ceton bom.

Shaidu sun ce a tashin farko mutum sama 70 aka yi jana’izarsu, idna wasu daga cikinsu tattara sassan jikinsu aka yi a buhu sannan aka binne.

’Ya’yana 6, duk an kashe su —Magidanci

Wani matashi, dan Tudun Biri, Idris Dahiru, ya ce, “Wannan jirgi ya kashe al’ummarmu maza da mata da yara a danginmu mun rasa mutum 34,”

Wani magidanci, Malam Musa, ya ce kanana 12 a gidansu harin ya kashe, ciki har da ’ya’yansa shida, maza uku da mata uku, da kuma ’ya’yan ’yan uwansa guda shida.

Shi ma wani Kirista da ya rasa ’ya’yansa biyu a harin, Solomon John ya ce ’ya’yan nasa na cikin Kiristoci uku da aka kashe a harin.

Ya ce yaran nasa, Kiristoci ne, amma suka halarci taron Mauludin, inda a nan suka gamu da ajalinsu.

Ya bayyana cewa al’ummar garin sun saba gudanar da tarukan Mauludi ba tare da wata matsala ba, sai a wannan karon.

Sarkin kauyen Ifira, daya daga cikin kauyukan da harin ya ritsa da mutanensu a taron, Malam Balarabe Garba, ya yi kira ga gwamnati ta biya diyyar wadanda harin jirign sojin ya shafa.

Al’umma da kungiyoyi na ci gaba da kira ga gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin gano abin da ya faru, da nufin hana aukuwar irin haka a nan gaba.

Sojoji da gwamnati sun amsa laifin

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta amsa ta cewar ita ce ta kai shi, amma bisa kuskure, inda babban  tsaro, Janar Christopher Musa, ya ba da tabbacin ba zai kara faruwa ba, da kuma alkawarin hukunta masu hannu a lamarin.

Haka shi ma Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa, Laftanar-Janar oreed Lagbaja, ya ba da tabbacin ba zai kara faruwa ba.

A nata bangaren, Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan tsaro,ta ba da tabbacin biyan diyya ga wadanda abin ya ritsa da su, da kuma hukunta wadanda ke da hannu a harin.

Jama’a sun fusata

Harin dai ya fusata ’yan Najeriya, ganin cewa shi ne irinsa na 16 a cikin shekaru, hudu.

Shararren malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda tsohon hafsan soji ne, ya yi zargin harin ba kuskure ba ne.

Hasali ma, sau biyu aka kai hari a ranar, inda suke cewa idan har na farko da an kai shi ne a bisa kuskure, na biyun da gangan aka kai shi.

Musamman ma ganin cewa daukacin hare-haren kuskuren da aka kai a cikin sun wakane da na Arewacin kasar.

Aminiya ta ruwaito daga yadda 2014 zuwa 2024 Jiragen Sojin Najeriya Suka kashe Fararen Hula 400 Bisa Kuskure.

Wannan mummunan hari ya sa jami’an gwamnati da yan shiyasa da sauransu suka yi ta zarya a Jihar Kaduna da ma kauyen Tudun Biri domin mika ta’aziyya da kuma dubiyar wadanda aka kwantar a asibiti.

Alkawarin tallafi

A irin wadannan ziyarce-ziyarce ne aka yi ta ba da gudunmmawa, inda Janar Lagbaja ya ba da Naira miliyan 10, da kuma cewa rundunar soji za ta dauki nauyin jinyar masara lafiyan, kodayake gwamnatin Kaduna da a tarayya sun riga sun dauki nauyi.

Kungiyar Gwamnonin Arewa ta ba da tallafin miliyan 180, Sanatoci suka ba da da gudummawar miliyan 1 kowannensu (N109m).

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya shaida wa Gwamna Uba Sani cewa sanatocin su 109 sun amince a ba da kudin daga albashin a matsayin gudunmuwa ga mutanen Tudun Biri

A nasu bangaren, ’yan Majalisar Wakilai ’yan Arewa, karkashin jagorancin Alhassan Ado Doguwa sun ba da gudunmmawar kudi Naira miliyan 45 da kayan more rayuwa na miliyan 350 da suka hada da cibiyar lafiya, azuzuwan makaranta da rijiyar burtsatse da kuma dakin taro a kauyen Tudun Biri.

Shi ma shugagaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya ba da umarnin a yi bincike a hukunta duk wadanda aka samu da laifi a harin, na daga cikin wadanda suka ba da tallafi tare da mataimakinsa, Kashim Shettima da ya wakilce shi.

‘Ba tallafi muke so ba’

Al’ummomi da kungiyoyi da daidaikun jam’a da suka harzuka da lamarin sun bayyana cewa hukunci suke so a dauka a kan duk masu hannu a harin.

Sannan gwamna ta biya cikakken diyya ga duk wadanda abin ya shafa tare da daukar nauyin iyalan da mamatan harin suka bari a baya.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin kasar ta biya cikakken diyya ga iylan.

Kungiyar Jama’atu Izalail Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah, ta bakin Sheikh Muhammad Sani yahaya Jingir, ya bukaci a biya diyya ga iyalan.

Haka shi ma babban malamin darikar tijjaniya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, da kuma mabia akidar Shi’a da kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar.

un a farko-farkon lamarin, Gwamnan Kaduna, Uba Sani dai a baana cewa an fara aaunawa da hukumomin da abin a shafa domin bian diar.

Zuwa kotu

Dukkanninsu kuma sun yi kira a a gudanar da cikakken bincike a hukunta duk jami’an sojin da aka samu da laifi ko sakacin da ya haddawa wannan bala’in.

A yayin da kungiyoyi ke kira da cewa wajibi ne a hukunta duk masu hannu a harin sannan a dauki matakan hana faruwar irin haka a nan gaba.

Daga cikin iyalan dai, tuni wani rukuni suka maka gwamnati da sojoji a kotu suna neman diyyar Naira biliyan 33.

Kazalika kungiyar lauyoyin Arewa ta lashi takobin zuwa kotu domin nema wa duk wadanda lamarin taba hakkokinsu.

Kwamitin tallafi

A halin da ake ciki dai Gwamnan Kaduna Uba Sani, ya sanar da kafa kwamitin gudanar da kudaden tallafin da aka ba wa iyalan gudunmmawa.

Abin da ake jiran gani shi ne yadda za a kai karshen wannan lamarin, musamman ganin yadda ’yan Najeriye ke cewa an dade ana ruwa kasa na shanyewa wajen gudanar da bincike kan abubuwan da suke faruwa, amma a karshe babu wanda ake hukuntawa.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna