Wata Ba-indiya ta yi barin ’yan 10

Wata Ba-Indiya ’yar shekara 28 da ke zaune a garin Madhya Pradesh ta yi barin ’yan 10 a dare daya. Matar mai suna Anju Kushwaha ta haifi jarirai tara a ranar Lahadin makon jiya, kafin a kaita asibiti, inda ta haifi  cikon na 10.Likitoci sun bayyamna cewa dauikacin jariran duk sun mutu ne a makon […]

Wata Ba-indiya ta yi barin ’yan 10
Wata Ba-indiya ta yi barin ’yan 10

Wata Ba-Indiya ’yar shekara 28 da ke zaune a garin Madhya Pradesh ta yi barin ’yan 10 a dare daya. Matar mai suna Anju Kushwaha ta haifi jarirai tara a ranar Lahadin makon jiya, kafin a kaita asibiti, inda ta haifi  cikon na 10.
Likitoci sun bayyamna cewa dauikacin jariran duk sun mutu ne a makon su na 12 a mahaifar uwa.
Akwai yiwuwar kwayoyin magani nasa kwayayen halitta suka taimaka wa Anju Kushwaha ta dauki cikin wadannan jarirai dab a taba jin mai yawansu ba, a cewar likitoci. Jaridar harkokin kasuwanci ta Business Standard, ta ruwaito cewa, wata cut ace ta rubanya kwayoyin halittar haihuwa da ake kira a Likitanci da “obarian hyperstimulation syndrome” ta haifarwa Ba-Indiyar bari a sanadiyya magunguna sanya haihuwa.
Saura kadan wannan mata da ta zama mace mafi yawan haihuwar  ’ya’ya masu yawa a duniya, amma a halin yanzu Nadya Suleman it ace wadda ke rike da kambi; ta haifi ’ya’ya takwas a shekarar 2009. Don haka Kundin abubuwan da suka shahar a duniya na Guiness book ya rubuta ta a matsayin wadda ta fi kowace mace yawan haihuwa a duniya.. Kodayake a shekarar 1971 an taba ciro wa wata mata ’yar shekara 35 ’ya’ya 15 a kasar Rum.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan