Wata cuta mai saurin kisan yara ta bulla Jihar Bauchi

Kimanin yara da dama ’yan kasa da shekara biyar ne suke rasuwa a garin Tiyin da ke cikin karamar Hukumar Warji a Jihar Bauchi, sakamakon bullar wani zazzabi mai tsanani da kuma tari, wanda har zuwa yanzu al’ummar garin da hukumomin kula da lafiya suka bayyana cewar ba su iya kai wa ga gano musabbabinsa, […]

Wata cuta mai saurin kisan yara ta bulla Jihar Bauchi

Kimanin yara da dama ’yan kasa da shekara biyar ne suke rasuwa a garin Tiyin da ke cikin karamar Hukumar Warji a Jihar Bauchi, sakamakon bullar wani zazzabi mai tsanani da kuma tari, wanda har zuwa yanzu al’ummar garin da hukumomin kula da lafiya suka bayyana cewar ba su iya kai wa ga gano musabbabinsa, illa dai kawai cutar na kashe yara da kuma galabaitar da su.

An sami kididdiga mabambanta na adadin yaran da suka rasa rayukansu cikin wata guda a wannan gari na Tiyin. Yayin da al’ummar ke hasashen alkalluman adadin yaran da suka rasu zuwa 100, wasu daga cikin shugabannin al’umma kuwa cewa suka yi yaran da suka rasu sun fi hamsin.

Sarkin Tiyin, Alhaji Shehu Idris ya roki Gwamnati da hukumomin kula da lafiya da su kawo masu agajin gaggawa domin ceto rayukan jama’ar yankin nasa domin shawo kan wanna cuta da ta fi kama yara ’yan kasa da shekara biyar.

Ya ce: “Idan yara sun harbu da cutar zazzabi mai tsananin zafin sai ka ga a cikin kwana daya ko biyu, wani lokacin ma a cikin wuni guda sai ka ji an ce yaro ya mutu da zarar zazzabin ya kama shi. Idan aka garzaya da yaro asibiti, nan take sai ka ji ana maganar karin jini, daga nan kuma maganar da za ta biyo baya shi ne yaro ya mutu. Haka muke fama, a cikin kasa da makonni uku yara sama da hamsin sun rasu.”

Ya kara da cewa: “Bayan zazzabi mai zafi da ke kama yaran, akwai kuma tarin nan na kata-kata, shi ma wannan ya addabi al’umma sosai. Ta kai ga tun ina jin koke-koken game da wadannan cututtuka guda biyu daga bakin masu rike da sarautun littafi da malamai yanzu abin ya kai ga hatta su mata da kansu suna zuwa gabana suna kokawa, don haka muke neman dauki.”

Ya ce suna fama da matsalar rashin hanya mai kyau, wanda shi ne dalilin da ya sa koda sun dauki yaro za a kai shi asibitin Gwaram na Jihar Jigawa da ke kusa. Haka ma waddnda ke garin Tiyin B suke kai majinyatansu Babban Asibitin Warji, nan ma haka suke fama da matsalar rashin hanya. Ya roki Gwamnatin Jiha da ta Tarayya da su zo da kwararru a duba, a ga abin da ke damun al’ummar, domin a taimaka masu.

A nasu bangaren cikin zantawar da suka yi da manema labarai daba-daban, al’ummar da ke zaune a yankin Tiyin A sun ce yawan yaran da suka rasu a yankinsu ya haura 54. Yayin da wadanda ke yankin Tiyin B suka ce wadanda suka rasu sun haura 30, sakamakon cutar zazzabi da tari.

Wadansu daga cikin iyayen da ’ya’yansu suka rasu sun ce sun rasa ’ya’ya hudu. Malam Musa Kaila, da ke zaune a Unguwar Kankare ya ce a gidansu yara hudu suka rasa, biyu ’ya’yansa ’yan shekara biyu da kuma uku, yara  biyu kuma na yayansa, saboda a cewarsa tarin yana shanye wa yara jinni ne. Ya kara da cewa, a gidan surukinsa ma akwai yara uku kwance rai a hannun Allah.

Ita Kuwa Malama Safiya ta ce ’ya’yanta guda biyu, Firdausi mai shekaru biyar da Aliyu mai watanni takwas a duniya. “Gaskiya na ji zafin rabuwa da ’ya’yana, domin da ba don tunanin kai ma kana tunanin makomarka ke nan ba, yarana kwanaki 15 ne kacal a tsakaninsu,” inji ta.

Limamin garin na Tiyin Malam Mika’ulu Yunusa, wanda shi ma ya rasa ’ya’yansa guda uku cur a sakamakon wannan cutar a cikin makonni uku, ya shaida cewar maganar zuwa jinya a asibiti kam gaskiya suna yi, amma masu kula da marasa lafiyar ne babu; don ya rasa yara uku a wannan cutar masu suna Azima, Nazifi da kuma Kamila.

Ya ce: “Ma’aikatan asibitin ba su cika zama ba, wani lokaci in ka je ba a cika samun kowa ba amma a bangarenmu muna kokarin fadakar da al’umma kan abin da ya da ce su yi.”

Binciken da wakilinmu ya yi, ya gano cewa akwai matsalar karancin ma’aikatan asibiti, kamar yadda al’ummar garin suka tabbatar. Shugaban hukumar kula da lafiya daga matakin farko na Jihar Bauchi, Pharmacy Adamu Ibrahim Gamawa ya ce sun sami labarin matsalar kuma tuni suka aike da kwamiti mai karfi domin ya binciko hakikanin mene ne ke addabar jama’ar garin na Tiyin da kuma shirin daukan matakin gaggawa,

Shugaban ya ce sun tabbatar da mutane 75 daga karamar Hukumar Warji sun kamu da cutar nan amma ba zai iya tabbatar da mutuwar yara da yawa ba. “Yanzu din nan da nake magana da kai, mun tura mutanenmu Warji domin su binciko mana mene ne ke akwai, saboda a asibiti ba mu sami rahoton rasuwa ba amma a cikin jama’a akwai saboda haka sai kwamitin ya binciko tukuna za mu gane abin da yake faruwa.

Domin wadanda suka mutu a cikin al’umma ba za mu gane mene ne ya kashe su ba, domin ba mu yi gwaje-gwaje a cikinsu ba, tilas sai an bincika. In Allah Ya so ’yan kwamitin da muka tura za su binciko mana kuma za mu yi aiki da rahoton da suka kawo mana nan take.” Kamar yadda shugaban ya bayyana wa Aminiya.