Wata cuta ta kashe dalibai takwas a Katsina
Wata cuta da ba a gano ta ba ta kashe dalibai takwas a makarantar sakandire ta garin Kurfi da ke Katsina. Wakilinmu ya gano cewa hukumomin makarantar kwanan ta rufe makarantar tare da tura daliban gida. Rufe makarantar bai yi wa ’yan majalisar jihar dadi ba inda ta bayyana kora daliban gida zai […]
Wata cuta da ba a gano ta ba ta kashe dalibai takwas a makarantar sakandire ta garin Kurfi da ke Katsina.
Wakilinmu ya gano cewa hukumomin makarantar kwanan ta rufe makarantar tare da tura daliban gida.
Rufe makarantar bai yi wa ’yan majalisar jihar dadi ba inda ta bayyana kora daliban gida zai iya ta’azzara batun.
Saboda haka majalisar ta ummarci kwamitinta na Ilimi da na Lafiya ya binciki batun.
Dan majalisa da ke wakiltar mazabar Kurfi, Kabir Lawal ya nemi zaburar da ’yan majalisar yayin da ya ankarar da su kan annobar cutar da kuma mace-macen da yara suka yi.