Wata cuta ta mai da budurwa tsohuwa
Wannan cuta tana sa yaro ko yarinya ninka shekarunsa ko shekarunta sau 4.
Wata budurwa mai suna Raizel Calago ’yar shekara 16 ce kawai, amma ba za a taba tsammani shekarunta ke nan ba idan aka ganta.
Budurwar tana fama da wata cuta da ba kasafai ake samun mutum da ita ba.
- Yawancin matan jami’a a Amurka na haifar ’yan gaba da Fatiha – bincike
- Zaben Shugabannin APC ya bar baya da kura a Jihohi da dama
Masana sun ce ana kiran wannan cuta progeria wadda take sa yaro ko yarinya ninka shekarunsa ko shekarunta sau 4.
A cikin shekara biyu kacal, Raizel ta tashi daga kyakkyawar budurwa, wadda ta taba halartar gasar sarauniyar kyau.
A yanzu halittarta ta sauya zuwa wata tsohuwa, har mutane da yawa suna kuskuren kiranta da sunan kakarta.
Matashiyar ’yar asalin kasar Filifin ta ce, ta fara lura da yamutsewar fatar jikinta, ’yan kwanaki sai wasu kuraje suka fito a duk jikin.
Jajayen alamomin kuraje suka bayyana mata, kuma lokacin da ta je duba lafiyarta, an gaya mata cewa kwari ne suka haddasa kurajen.
An ba ta magani, amma hakan bai yi tasiri ba, kuma ba da dadewa ba, ta fara lura da canje-canje a jikinta.
Yanzu, yana da wahala a yi imani ita ’yar shekara 16 ce kawai.
“Abin takaici ne lokacin da aka gaya min cewa, ’yata ta girme ni.
“Wani lokaci, ina tunaninta lokacin da ta tsufa kuma na ga yadda za ta yi kyau,” inji mahaifiyar Raizel, mai suna Joela mai shekara 36.
“Tana da kyau tun tana jaririya, amma yanzu fuskarta, ta yi nisa da kyanta lokacin tana karama.”
Tun lokacin da kamanninta suka canja, budurwar mai shekara 16 tana jin kunyar yin cudanya da kawayenta kamar yadda ta saba.
Ta kuma guji fita ba tare da abin rufe fuska ba. Yawancin fuskarta a rufe, saboda tana jin kunyar yadda ta kasance.
Abin da kawai take so shi ne; jikinta ya koma yadda yake shekarun da suka gabata.