Wata da aka yi wa fyade ta rasu bayan shekara 42 a sume (2)

A ranar Litinin da ta gabata ne wata mata ’yar kasar Indiya da aka yi wa fyade a shekarar 1973 ta rasu, bayan da shafe shekaru 42 cikin doguwar suma. Matar mai suna, Aruna Shanbaug, mai kimanin shekaru 67, ta rasu ne da misalin karfe takwas da rabi na safiya agogon kasar, a wani asibiti […]

Wata da aka yi wa fyade ta rasu bayan shekara 42 a sume (2)
Wata da aka yi wa fyade ta rasu bayan shekara 42 a sume (2)

A ranar Litinin da ta gabata ne wata mata ’yar kasar Indiya da aka yi wa fyade a shekarar 1973 ta rasu, bayan da shafe shekaru 42 cikin doguwar suma.

Matar mai suna, Aruna Shanbaug, mai kimanin shekaru 67, ta rasu ne da misalin karfe takwas da rabi na safiya agogon kasar, a wani asibiti da ke birnin Mumbai, kamar yadda gidan talabijin na CNN ya ruwaito. Kafin rasuwar marigayiyar, ma’aikaciyar jinya ce a asibitin da ta yi jinya. Shugaban asibitin Dokta Abinash Supe ya ce ta mutu ne sakamakon ciwon masassarar Nimoniya da kuma ciwon zuciya.
“An sanya Aruna akan na’aurar da ke taimaka mata wajen lumfashi duk tsawon wadannan shekaru. Hakazalika, ana ba ta abinci ne ta roba. Kuma ta kasance cikin yanayin doguwar suma har na tsawon shekaru 42 da ta yi jinya,” inji shi.
A shekarar 2000 wani marubuci kuma dan jarida, mai suna, Pinki birani da ke zaune a birnin Mumbai, ya rubuta wani littafi mai suna, “Labarin halin da Aruna take ciki.” Kuma kamar yadda marubucin ya yi ikirari a littafin ya ce wani mai aikin shara ne a asibitin da take aiki ya yi mata fyade bayan ya daure ta da sarka.
Kodayake, a ranar 7 ga watan Maris din shekarar 2011 ne, Mista Pinki ya gabatar da bukatar a gaban Kotun kolin kasar Indiya, inda yake kira da kotun da bai wa likitoci umarnin kawo karshen rayuwar Aruna ta hanyar yi mata allurar guba. Amma sai kotun ta ki amincewa da bukatar da ya gabatar.