Wata daya kafin zabe, Kotu ta haramta wa Elisha Abbo takarar Sanata a APC
Kotun ta ce APC ta kori Sanata Abbo a gundumarsa
Babbar Kotun Jihar Adamawa mai zamanta a Yola, babban birnin jihar, ta cire Sanata Elisha Abbo daga matsayin dan takarar Sanata na jam’iyyar APC a mazabar Adamawa ta Arewa a zaben 2023.
Wannan na zuwa ne yayin da ya rage kwana 46 kafin zaben na 2023.
- Kotu ta daure matashi shekara 3 kan satar abin wanke-wanke
- ‘Buhari zai kaddamar da jirgin saman da aka kerawa a Najeriya kafin ya bar mulki’
Jaridar Politics Nigeria ta rawaito kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Danladi, ta cire Sanata Abbo ne bisa dalilin jam’iyyarsa ta kore shi daga matakin gundumarsu da ke Karamar Hukumar Mubi ta Arewa a jihar.
Alkalin ya ce Sanatan da APC na karkashin duk hukuncin da Majalisar Zartarwar jam’iyyar reshen Karamar Hukumar Mubi ta Arewa ta yanke na korarsa daga jam’iyyar a ranar 7 ga watan Oktoba, 2022.
Haka nan, kotun ta ce Sanata Abbo ba shi da ’yancin cin moriyar wata damar da mambobin jam’iyyar APC ke samu.
Idan za a iya tunawa, a ranar 7 ga Oktoban 2022, Shugabannin APC na Karamar Hukumar Mubi ta Arewa suka kori Sanata Abbo daga jam’iyyar kamar yadda kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ya ba da shawara.
Kotun dai ta haramta wa APC a yankin ta riki Abbo a matsayin dan takararta, tana mai cewa ba shi da hurumin sabunta takararsa karkashin jam’iyyar balle ya shiga zabe mai zuwa.