Wata giwa a kasar Sin ta kashe mace, ta farmaki dan sanda
Yan sanda sun samu gungun wasu giwayen nahiyar Asiya 14 a dajin dishuangbanna da ke gundumar Yunnan, inda aka samu gawar wata mata a ranar Asabar din da ta gabata, kamar yadda shafin sadarwar Jihar Yunnan Wang ya bayyana.“Binciken farko da aka gudanar, ya nuna cewa giwaye ne suka farmaki matar,” a cewar Kamfanin Dillancin […]
Yan sanda sun samu gungun wasu giwayen nahiyar Asiya 14 a dajin dishuangbanna da ke gundumar Yunnan, inda aka samu gawar wata mata a ranar Asabar din da ta gabata, kamar yadda shafin sadarwar Jihar Yunnan Wang ya bayyana.
“Binciken farko da aka gudanar, ya nuna cewa giwaye ne suka farmaki matar,” a cewar Kamfanin Dillancin Labaran kasar sin na dinhua.
Shafin Yunnan Wang ya bayyana cewa gungun masu binciken “:sun hadu da matsala, don haka suka yi gagawar barin wurin,” lokacin da giwayen suka kai musu farmaki.
Wannan daji dishuangbanna, na kan iyakar kasar Sin da Myanmar da Laos, inda dandanzon giwaye da yawansu ya kai 250 zuwa 300 suke zaune, a cewar dinhua.
Dabbobi suna zaune cikin aminci, amma akwai yiwuwar sukai farmaki da zarar sun ga wani abu da ke barazana ga rayuwarsu. A shekarar 2010, giwaye sun kashen wani mutum a lokacin da yake tsinkar barkono a dishuangbanna, kamar yadda shafin sadarwar dinhuanet ya ruwaito.