Wata Hajiyar Zamfara ta haihu a cikin jirgi
A ranar Litinin da ta gabatab wata Hajiya daga Jihar Zamfara ta haihu a cikin jirgin sama a filin jirgi na Sarki Abdul’azeez da ke Jiddah a kan hanyarsu ta dawowa Najeriya. Rahotanni daga filin jirgin sun ce Hajiyar wadda aka sakaye sunanta tana zaune tare da alhazan jihar a cikin jirgi suna jiran tashi […]
A ranar Litinin da ta gabatab wata Hajiya daga Jihar Zamfara ta haihu a cikin jirgin sama a filin jirgi na Sarki Abdul’azeez da ke Jiddah a kan hanyarsu ta dawowa Najeriya.
Rahotanni daga filin jirgin sun ce Hajiyar wadda aka sakaye sunanta tana zaune tare da alhazan jihar a cikin jirgi suna jiran tashi zuwa Najeriya sai nakuda ta kama ta, inda kafin a kai ta asibiti kan jariri ya bullo, kuma hakan ya sa tilas babu yadda za a illa a bari ta haihu a cikin jirgin.
Wasu likitoci hudu da ke tare da Alhazan a cikin jirgin ne suka taimaka wa Hajiyar yayin haihuwa daga bisani aka kai ta wani asibiti a Jiddah domin ci gaba da kula da ita.
Wani jami’in Jihar Zamfara da ke cikin wadanda suka taimaka wa matar da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, “Bayan mun saka alhazanmu dukka a cikin jirgi a ranar Litinin da misalin karfe 2:00 na dare sai na koma na kwanta su kuma suna jiran jirgi ya tashi da su zuwa Najeriya, da na farka da safe sai na ji wai daya daga cikin alhazanmu mace ta haihu a cikin jirgi kafin ya tashi. Allah Ya taimaka akwai ma’aikatan lafiya hudu da ke cikin jirgin lokacin da ta soma nakuda kuma su ne suka taimaka ta haihu daga baya aka kai ta wani asibiti a nan garin Jiddah.” Ya tabbatar da cewa uwar da jaririn duk suna cikin koshin lafiya.
Idan ba a manta ba kwanakin baya ne alhazai biyu daga Jihar Zamfara suka haihu a birnin Makkah kuma hakan ya saba wa dokar Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), inda ta sha alwashin hukunta jihar ta hanyar rage yawan kujeru da za a ba ta a badi saboda barin masu juna biyu sun je aikin Hajji.