Wata irin cutar kwayar halitta ta bayyana a Kano

Likitoci a asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, sun gano wata irin cutar kwayar halitta, wadda a Turancin Kimiyya ake yi lakabi da  Warrdenburg Syndrome. Wannan cuta na illata ji da sauya launin idanu da gashin kai, kamar yadda aka gano a cikin mutum 12 da suka fito daga zuri’a guda, wadanda ke zuane a […]

Wata irin cutar kwayar halitta ta bayyana a Kano
Wata irin cutar kwayar halitta ta bayyana a Kano

Likitoci a asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, sun gano wata irin cutar kwayar halitta, wadda a Turancin Kimiyya ake yi lakabi da  Warrdenburg Syndrome. Wannan cuta na illata ji da sauya launin idanu da gashin kai, kamar yadda aka gano a cikin mutum 12 da suka fito daga zuri’a guda, wadanda ke zuane a Jihar.
kwararrun masana harkar kula da lafiya sun bayyana cewa, gano wannn kwayar cutr halitta wadda ke da nasaba da gado, ba ta da magani, domin haka take yaduwa a cikin zuri’a. Don haka akwai bukatar yin bincike kafin aure, tamkar yadda ake bai wa masu cutar laujen jini, ta “sickle cell.”
Wannan cutar kwayoyin halitta ta “warrdenburg syndrome,” ana samunta ne a jikin mutum daya cikin mutum dubu 40, ko kuma mutum daya cikin kurame 30. Wannan cuta ta samo aslain sunanta ne daga wani kwararren likitan ido, mai suna Petrus Johannes Warrdenburg.
Alamun wannan cuta sun hada da kurumta ko bebentaka da faci-facin farin gashi a gaban goshi da shudin ido da furfura a lokacin kuruciya da kuma toshewar hanci.
Shugaban Sashen kula da lafiyar Kunne da hanci da makoshi (ENT), na asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano (AKTH). Dokta Kolo Emmanuel, ya bayyana cewa sau daya asibitin ya taba gano irin wannan cuta a tsawon shekara shida, inda ya bayyana yadda suka gano al’amarin cutar a wannan karo da cewa abin mamaki ne.
Dokta Emmanuel tare da abomkin aikinsa, Dokta abdulAzez, wadanda ke duba majiyatan da ke fama da cutar sun bayyana cewa, zuri’ar da ke fama da cutar, sun kamu ne rukunin farko na cutar (wato Type I)
Sai dai wani masanin a fannin kula da lafiyar kunne da hanci da makoshi (ENT), Dokta Salisu AD, ya bayyana cewa, gano wannan cuta da aka yi ba yana nufin ta fara bazuwa ba ne. Kuma ya bukaci a wayar da kan jami’an kula da lafiya game da cutar, ta yadda da su ga majiyacin da ke fama da irin cutar za su iya ganewa, su kuma tura shi inda ya kamata ya samu cikakkiyar kulawa.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda