Wata kotu ta ci tarar matar da ta zagi mijinta a waya tarar Naira dubu 500
Kotun daukaka kara ta Khor Fakkan da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ci tarar wata mata da ta zagi mijint aa waya Dirhami 5,000, watoi daidai da Naira dubu 500. ’Yan sandan Khor Fakkan sun samu korafi da wani mutum, wanda ya zargi matarsa da zaginsa, tare da wulakanta shi a waya. Bai […]
Kotun daukaka kara ta Khor Fakkan da ke kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta ci tarar wata mata da ta zagi mijint aa waya Dirhami 5,000, watoi daidai da Naira dubu 500.
’Yan sandan Khor Fakkan sun samu korafi da wani mutum, wanda ya zargi matarsa da zaginsa, tare da wulakanta shi a waya. Bai ram aba, don hakaya yanke matsaya wajen kai kara a wajen ’yan sanda.
Matar dai ta amince da cewa ta tafka kuskure, amma ta yi togaciya da cewa fushi da bacin zuciya ner suka ingizata.