Wata kotu ta haramta sa nikabi a Faransa

Wata kotu a Faransa ta jaddada hukuncin haramta sanya nikabi a bainar jama’a a kasar bayan daukaka karar da wata mata ta yi a gabanta kan hakkinta na bin addinin da ta so. Hukuncin kotun garin Strasbourg shi ne na biyu tun bayan da kasar Faransa ta kafa dokar a shekarar 2010 wadda ta haramta wa […]

Wata kotu ta haramta sa nikabi a Faransa
Wata kotu ta haramta sa nikabi a Faransa

Wata kotu a Faransa ta jaddada hukuncin haramta sanya nikabi a bainar jama’a a kasar bayan daukaka karar da wata mata ta yi a gabanta kan hakkinta na bin addinin da ta so.
 Hukuncin kotun garin Strasbourg shi ne na biyu tun bayan da kasar Faransa ta kafa dokar a shekarar 2010 wadda ta haramta wa mata sanya nikabin don boye fuska a bainar jama’a ciki har da titunan kasar. Dokar dai ta fara aiki ne a shekarar 2011.
Alkalin kotun ya yi watsi da karar da matar Musulma mai shekara 20 da ’yan kai ta shaida wa kotun cewa ba a kodayaushe ne take boye fuskar ta ba, amma kuma duk lokacin da ta yi hakan ta yi ne domin bin koyarwar addininta.
Cikin masu sukar dokar har da masu rajin kare hakkin dan Adam wadanda suke cewa dokar tana nuna kyama ne ga addinin Musulunci da Musulmai.  A karkashin dokar dai duk macen da aka kama ta sanya nikabi, za ta fuskanci tara da ta kai Dala 205 (Kimanin Naira dubu 34)
kasar Faransa ce dai ta fi yawan Musulmi a yankin Yammacin Turai wadanda suka kai kimanin miliyan biyar  wanda hakan ya sa batun ya zama wani abu da ke daukar hankali sosai. Kuma matakin dokar ya sanya ta cikin sahun kasashen nahiyyar Turai kalilan da suka haramta sa nikabi. Sauran kasashen sune: Netherlands da Belgium.