Wata kotu ta sake bayar da umarnin kamo tsohon Ministan Lantarki Saleh Mamman

A makon da ya gabata ne wata Babbar Kotun Tarayya ta kama Saleh Mamman da laifin karkatar da kuɗaɗen ayyukan tashoshin samar da wutar lantarki na Zungeru da Mambilla.

Wata kotu ta sake bayar da umarnin kamo tsohon Ministan Lantarki Saleh Mamman

Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama a Abuja ta bayar da umarnin kamo tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, bayan ya gaza halartar zaman shari’ar da ake yi masa kan zargin almundahana ta Naira biliyan 31.

Rashin halartar kotun da Saleh Mamman ya yi a ranar Litinin ya sa Mai Shari’a Maryanne Anenih, ta ɗage shari’ar zuwa ranar Alhamis.

Wannan ne karo na biyu cikin kwanaki kaɗan da kotu ke bayar da umarnin kama shi, bayan wata kotu a Abuja ta same shi da laifin karkatar Naira biliyan 33.8 a wani shari’ar ta daban a ranar 7 ga watan Mayu.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Saleh Mamman tare da wasu mutum bakwai kan zargin haɗa baki da karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin ayyukan wutar lantarki.

Duk sauran waɗanda ake tuhuma sun halarci zaman kotun na ranar Litinin, yayin da Saleh Mamman bai je ba.

Lauyan gwamnati, Rotimi Oyedepo, ya roƙi kotu ta bayar da umarnin kama shi tare da ci gaba da shari’ar duk da rashin zuwansa, kuma kotun ta amince.

Tun a makon da ya gabata ne wata Babbar Kotun Tarayya ta kama Saleh Mamman da laifin karkatar da kuɗaɗen ayyukan tashoshin samar da wutar lantarki na Zungeru da Mambilla.