…Wata kuma ta daba wa mijinta fasasshiyar kwalba a Zamfara
Wata matar aure mai suna Hauwa’u ta daba wa mijinta fasasshiyar kwalba a kirji da baya a unguwar Filin Jirgi da ke Gusau a Jihar Zamfara. Kakakin Asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau, Awwal Usman Ruwan dorawa ya tabbatar wa wakilinmu cewa an kai mijin mai suna Bilyaminu Yusuf asibitin, kuma yana samun […]

Wata matar aure mai suna Hauwa’u ta daba wa mijinta fasasshiyar kwalba a kirji da baya a unguwar Filin Jirgi da ke Gusau a Jihar Zamfara.
Kakakin Asibitin kwararru na Yariman Bakura da ke Gusau, Awwal Usman Ruwan dorawa ya tabbatar wa wakilinmu cewa an kai mijin mai suna Bilyaminu Yusuf asibitin, kuma yana samun sauki.
“Na ga majinyacin lokacin da aka kawo shi nan, kuma ba ya iya yin magana saboda yana cikin mawuyacin hali. Singiletinsa ta yi caba-caba da jini. ’Yan uwansa sun shaida min cewa ma’auratan sun samu sabani lokacin da ya ki karbo belin dan uwanta da yake tsare a hannun ’yan sanda, don haka matar ta fusata ta daba masa fasasshiyar kwalba,” inji Ruwan doruwa.
Wata majiyar ta shaida wa Aminiya cewa, ma’auratan sun yi aure ne shekara takwas da suka gabata, amma Allah bai albarkace su da haihuwa ba. Majiyar ta ce lokacin da mijin ya nuna zai kara aure sai ta daburce masa ta sha alwashin za ta yi maganinsa.
Matar dai ta gudu bayan da ta daba masa kwalbar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Zamfara, DSP Muhammad Shehu ya ce, tuni sun kama Hauwa’u kuma sun fara bincike a kai.
Wannan lamari na Zamfara ya zo ne kwanaki kadan da kashe Bilyaminu Bello dan tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP ta kasa Alhaji Bello Halliru da ake zargin matarsa Maryam Sanda ’yar tsohuwar Shugaban Bankin Aso Sabings and Loans Plc, Hajiya Maimuna Aliyu da aikatawa.