Wata kungiya ta ja kunnen Sanata Kwankwaso

kungiyar tuntuba da ci gaban ’yan Arewa (AYF) ta nuna rashin jin dadinta da irin kalaman da suka fito daga bakin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a lokacin da ya ziyarci Legas domin karbar belin matasa ’yan Arewa da aka kama a dalilin rikicin kasuwar Mil 12 a kwanan baya.“Ba mu ji […]

Wata kungiya ta ja kunnen Sanata Kwankwaso
Wata kungiya ta ja kunnen Sanata Kwankwaso

kungiyar tuntuba da ci gaban ’yan Arewa (AYF) ta nuna rashin jin dadinta da irin kalaman da suka fito daga bakin tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a lokacin da ya ziyarci Legas domin karbar belin matasa ’yan Arewa da aka kama a dalilin rikicin kasuwar Mil 12 a kwanan baya.
“Ba mu ji dadin kalaman da ya yi ba, domin alama ce ta barin baya da kura.” Inji shugaban kungiyar, Alhaji Shettima Yerima, wanda ya kara da cewa: “A lokacin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya isa Legas, ya kasa yin aiki da siyasa wajen kai gaisuwar ban girma ga Oba na Legas da Gwamnan Jihar, sai kawai ya yi gaban kansa na karbar belin matasan da ke tsare. Kuma a gaban jama’a ya yi ta fadin kalamai da za su kara ruruta gabar kabilanci a tsakanin mutanenmu da jama’ar gari; wanda bai dace irin wadannan kalamai su rika fitowa daga bakin shugaban al’umma ba.”
“Mai martaba Oba na Legas ya nuna matukar bakin ciki da irin kalaman da ya jiye wa kunnuwansa a cikin hoton bidiyo da aka kai masa, wanda Sarkin Hausawan Legas Alhaji Aminu Dogara ya hanzarta zuwa fadar Oban domin tausarsa da ba shi hakuri. Ka ga wannan alama ce ta barin baya da kura, domin ya zo ya fadi abin da yake so ya bar mu cikin jangwam. Saboda haka muke gargadin shi da kada ya mayar da rikicin kasuwar Mil 12 ya zama dandalin siyasa na yakin neman zaben kujerar Shugaban kasa da yake shirin fitowa a shekara ta 2019. Kuma nasarar da jam’iyar APC ta samu a zaben da ya gabata a Legas, ya samu ne a dalilin shaidar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu na dattaku da kishin kasa da ci gabanta. Idan har Kwankwaso yana da sha’awar fitowa a shekarar 2019, to sai ya yi koyi da irin wadannan halaye na neman hadin kan al’ummar kasa amma ba kirkiro hanyar kulla gaba tsakanin al’umma da Kwankwaso yake yi ba.”
Ya ci gaba da cewa: “A gaskiya ba mu ji dadin irin cin fuska da Sanata Kwankwaso ya yi wa Gwamnan Jihar Legas da Oba na Legas ba. Ya kamata sauran jama’a ’yan Arewa su goyi bayan matakin da muke dauka a kan Kwankwaso wanda ya wulakanta shugabannin Yarabawa a bainar jama’a kuma a cikin masarautarsu. Muna so Kwankwaso ya fito ya nemi gafarar wadannan shugabanni tun da wuri, domin ya tsame mu daga kyamatar da ake yi mana a wannan sashe.”