Wata kungiya ta raba kayayyakin abinci ga ’yan gudun hijira a Azare

A ranar Alhamis din makon jiya ne kungiyar Kula da Marasa Galihu da Tallafa wa Marayu ta karamar hukumar Katagum a Jihar Bauchi ta raba dimbin kayayyakin abinci ga ’yan gudun hijirarda suka fito daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa da suke zaune a garin Azare da karamar hukumar.Wadanda aka raba musu kayayyakin sun […]

Wata kungiya ta raba kayayyakin abinci ga ’yan gudun hijira a Azare
Wata kungiya ta raba kayayyakin abinci ga ’yan gudun hijira a Azare

A ranar Alhamis din makon jiya ne kungiyar Kula da Marasa Galihu da Tallafa wa Marayu ta karamar hukumar Katagum a Jihar Bauchi ta raba dimbin kayayyakin abinci ga ’yan gudun hijirarda suka fito daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa da suke zaune a garin Azare da karamar hukumar.
Wadanda aka raba musu kayayyakin sun hada da maza da mata da kananan yara, kuma wannan ne karon farko da kungiyar taraba kayayyakin tallafin a yankin.
Da yake zantawa da Aminiya a wajen rabon kayayyakin Shugaban kungiyar Kwamared Sa’idu Dahuwa Azare ya ce tun lokacin da suka kafa kungiyar kusan kullum sai ya samu dimbin mata ’yan gudun hijira a kofar gidansa suna neman taimakon kayan abinci don haka suka bude asusun neman taimako amma ’yan kadan ne daga cikin al’umma suka taimaka.
Kayayyakin da aka raba wa ’yan gudun hijirar sun hada da taliyar Indomi da taliya da garin sabulun wanki da sabulun wanka da na wanki da garin masara da gishiri sai yaduddukan shadda da littattafan karatu.  Sauran sun hada da gero buhu 15 da shinkafa buhu biyar da takalman yara.
Ya ce kashi 95 cikin 100 na ’yan gudun hijirar yankin mata ne da kananan yara da iyayensu suka kwanta dama sakamakon rikicin Boko Haram a jihohin Borno da Yobe da Adamawa musamman karamar Hukumar PotiskumShugaba kungiyar ya ce sun kashe kimanin Naira dubu 280 wajen sayo kayayyakin, kuma ya ce sama da mutum 260 suka amfana da kayayyakin tallafin inda ya yi fatar al’ummar yankin za su ci gaba da ba kungiyar goyon baya don inganta rayuwar marasa galihu a yankin.
Ya ce ’yan kasuwa daidaiku ne suka ba da gudunmawar kudin da suka sayi kayayyakinkuma akwai wasu ’yan siyasa biyu da suka ba da gudunmawa.
Ya ce Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Bauchi (SEMA) ta yi alkawarin za ta ba da gudunmawa amma har zuwa wannan lokaci babu abin da suka ba su a hukumance.
“Muna ba da hakuri ga wadanda ba su samu tallafi a wannan karon ba, za mu ci gaba da neman taimako domin mun san halin da mutane suke ciki na mawuyacin hali,” inji Kwamared Dahuwa
Ya ce “Yanzu haka mun yi rijistar sama da mutum 1600 kuma kusan kullum sai mun samu sababbin mambobi a wannan kungiyar.”