Wata kungiya ta tallafa wa iyalai 67,106 da kayan abinci a Katsina

Iyalai 67,106 da ke cikin matsananciyar bukata sakamakon annobar COVID-19 a Jihar Katsina za su samu kayan tallafi daga. Gwamnan Jihar Aminu Masari, yayin kaddamar da rabon tallafin da kungiyar COCOVID-19 ta bayar domin raba wa mabukata a jihar. Ya ce kowannen daga cikin iyalan da aka riga aka tantace zai samu masara da shinkafa […]

Wata kungiya ta tallafa wa iyalai 67,106 da kayan abinci a Katsina

Wani sashe na kayan abincin da Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Farouk, ta mika wa gwamnatin jihar Kano. (Tsohon hoto)

Iyalai 67,106 da ke cikin matsananciyar bukata sakamakon annobar COVID-19 a Jihar Katsina za su samu kayan tallafi daga.

Gwamnan Jihar Aminu Masari, yayin kaddamar da rabon tallafin da kungiyar COCOVID-19 ta bayar domin raba wa mabukata a jihar.

Ya ce kowannen daga cikin iyalan da aka riga aka tantace zai samu masara da shinkafa da taliya da da gishiri da kuma taliyar zamani.

Wakilin COCOVID-19, Bello Mohammed ya ce kayan na daga cikin kokarin kungiyar na rage wa talakawa matsin da annobar ta jefa su a ciki.

Gwamnan Jihar ya ce za a tsaurara matakan tabbatar gaskiya a rabon kayan ta hanyar amfani da sarakuna da kungiyoyin kare hakkin dan Adama da sauran masu ruwa da tsaki.

Masari wanda ya ce annobar coronavirus ta tilasta wa gwamnatinsa takaita ayyuka a wasu bangarori, ya kara da cewa suna sun iya kokarinsu domin shawo kan cutar da kuma yin wasu ayyuka.