Wata kungiya ta tuhumi Amitabh Bachchan da haddasa kisan mutane
Wata kungiyar mabiya addinin Sikh a Amurka ta kai karar shahararren dan fim din Indiya, Amitabh Bachchan ga hukumomin kasar Australia, inda suka tuhume shi da hannu wajen haddasa hargitsin nuna kyama ga mabiya addinin Sikh a watan Nuwamban shekarar 1984, a kasar, wanda a sakamakon rikicin, mutane da dama mabiya addinin na Sikh suka […]
Wata kungiyar mabiya addinin Sikh a Amurka ta kai karar shahararren dan fim din Indiya, Amitabh Bachchan ga hukumomin kasar Australia, inda suka tuhume shi da hannu wajen haddasa hargitsin nuna kyama ga mabiya addinin Sikh a watan Nuwamban shekarar 1984, a kasar, wanda a sakamakon rikicin, mutane da dama mabiya addinin na Sikh suka mutu, wasu kuma suka samu munanan raunuka.
An shigar da karar ce a Talatar da ta gabata, a daidai lokacin da dan wasan yake a kasar ta Australia, inda ya je da nufin amsar digirin girmamawa da Jami’ar Kimiyya ta kueensland ta birnin Brisbane ta ba shi.
A tuhumar, wacce ta hadin gwiwa ce tsakanin kungiyar addinin Sikh da ke Amurka da kuma kungiyar daliban kasar Indiya mabiya addinin Sikh, kamar kuma yadda ta hada da dukkan iyalan wadanda suka rasu ko suka jikkata a sakamakon hargitsin da ya faru a 1984.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta intanet Khaleej Times ta ruwaito, mai ba kungiyar mabiya addinin Sikh a Amurka shawara ta fuskar shari’a, Gurpatwant Singh Pannun ya ce akwai sashin dokokin kasar Australia da ya ba da damar a tuhumi mutum koda ba a kasar ya aikata laifin ba, madamar yana halarce a kasar, lokacin da aka shigar da karar.