Wata kungiya ta yaba da kokarin hukumar PCNI

Mataimakin Shugaban hukumar PCNI, Tijjani Tumsah ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai duba hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin da al’umma ke fuskanta a Arewa Maso Gabas. Ya bayyana haka ne a lokacin da wakilan wata kungiya mai tausaya wa al’ummar yankin na Arewa Maso Gabas suka ziyarce shi a ofishinsa […]

Wata kungiya ta yaba da kokarin hukumar PCNI

Mataimakin Shugaban hukumar PCNI, Tijjani Tumsah ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai duba hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin da al’umma ke fuskanta a Arewa Maso Gabas. Ya bayyana haka ne a lokacin da wakilan wata kungiya mai tausaya wa al’ummar yankin na Arewa Maso Gabas suka ziyarce shi a ofishinsa da ke Abuja. A lokacin da yake nuna masu taswira da jaddawalin yadda za a sake gina yankin da yakin Boko Haram ya lalata, ya yaba wa kungiyar saboda kokarinsu na kawo hadin kai ga al’ummar yankin. Ya ce an kafa Hukumar PCNI ne da nufin tattara tallafi da kawo hanyoyin da za a sama wa al’ummar yankin sauki daga radadin ibtila’in da suke fuskanta. Ya ce za su hada hannu da kungiyar domin cin ma nasara.

Shugaban kungiyar ta tausaya wa al’ummar Arewa Maso Gabas, Hon. Muhammad Kumaliya ya yaba da kokarin hukumar PCNI na sake gina yankin wanda ya fuskanci matsalolin ta’addanci. Ya ce makasudin kungiyar tasu shi ne su bayyana wa hukumar kudurori da manufofinta, wadanda suka ta’allaka ga sake ginawa da raya yankin Arewa Maso Gabas. Ya ce yankin yana da karsashin da zai ci gaba da tallafa wa kasar nan wajen bunkasa tattalin arziki, amma ya ce a sanadiyyar yakin nan, ya haifar masu da koma baya a sanadiyyar mace-mace da asarar dukiya da sauransu. Ya ce kungiyar tasu a shirye take ta ci gaba da wayar da kan al’umma domin samar da hadin kai ga al’ummar Arewa Maso Gabas. Ya gode da irin salon mulkin Buhari da kuma hukumar PCNI domin jajircewarsu wajen aikin lantarki na Mambila. Ya yi rokon a maida hankali a tabbatar an kammala aikin cikin lokaci domin amfanin al’umma gaba daya. daya daga cikin membobin kungiyar, Hon. Adamu Modibbo, ya bayyana cewa suna nan suna shirin hada babban taron masu ruwa da tsaki da masana, domin tattauna hanyoyin bunkasawa da gina yankin na Arewa Maso Gabas cikin sauri, kamar yadda Shugaban kasa Buhari ya kudurta.