Wata kungiya za ta yi amfani da na’ura don gano masu fyade
kungiyar nan da ke rajin yaki da cin zarafin ‘ya’ya mata da kananan yara da ke Jihar Kano ta bayyan cewa a shirye take ta fara amfani da na’urar binciken halittar dan adam ta DNA don gano masu fyade a fadin jihar. kungiyar ta bayyana cewa a kwanakin baya ne Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano […]
kungiyar nan da ke rajin yaki da cin zarafin ‘ya’ya mata da kananan yara da ke Jihar Kano ta bayyan cewa a shirye take ta fara amfani da na’urar binciken halittar dan adam ta DNA don gano masu fyade a fadin jihar.
kungiyar ta bayyana cewa a kwanakin baya ne Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano Honorabil Abdullahi Yusuf Ata ya yi wa kungiyar alkawarin samar da na’urar da ke binciken kwayar halittar dan adam ta DNA.
Sakataren kungiyar Alhaji Abbas Ibrahim ne ya bayyana haka a shirin Barka da Hantsi na gidan Rediyon Freedom. Alhaji Abbas ya ce samar da wannan na’ura zai taimaka wajen gano masu
laifi kowane iri cikin sauki wanda ya ce tuni kasashen da suka ci gaba suka fara amfani da wannan na’ura. “Na’ura ce da ke binciken kwakkwafi idan an yi laifi ba wai kawai na fyade ba naura ce da ke gano halittar dan adam a yanzu haka kmaar yadda Shugaban majalisar dokokin Jihar Kano ya ba mu tabbaci za a samar da wannan na’ura duba da cewa duk fadin kasar nan Jihar Legas ce kadai ke da wannan na’ura, kodayae su ma bai wuce wata daya da suak same ta ba. Wannan na’urar za ta saukaka binciken laifuffuka musamman ma abin da ya shafi fyade”.
Ita ma anata tsokacin mamba a cikin kungiyar, wacce a hannu guda kuma ita ce Sakatariyar kungiyar Lauyoyi Mata ta Jihar Kano, Barista Huwaila Ibrahim Ahmad ta bayyana cewa samar da na’urar zai taimaka wajen rage matsalolin fyade da ya addabi al’umma a Jihar Kano “batun
yadda ma muke bincikenmu ada muna samun matsala, domin za ki ga idan an sami fyaden nan tun kafin aje ko’ina za ki ga iyaye sun wanke wa yarinyar jiki, anan komai na shaida ya tafi. Amma da samuwar na’urar zan iya cewa tabbas indai aka kama mai laifi za a tabbatar da cewa shi ne ya aikata laifin.”
Baristar ta kuma yi kira ga iyaye da su kara kaimi wajen sanya wa ‘ya’yansu ido don a samu a dakile matsalar fyaden a tsakanin al’umma.