Wata kungiyar matasa ta jawo cece-ku-ce a Dambatta

Wata kungiyar matasa mai suna kungiyar Ci Gaba ta Mazaje a garin Dambatta Jihar Kano, ta jawo cece-ku-ce sakamakon fassara daban-daban da mutane suke yi mata, sakamakon karar da wata budurwa ’yar kungiyar ta kai ofishin Hisbah na garin.Wani da ba ya son a bayyana sunansa ya ce ’ya’yan kungiyar matasa ne zalla da ba […]

Wata kungiyar matasa ta jawo cece-ku-ce a Dambatta
Wata kungiyar matasa ta jawo cece-ku-ce a Dambatta

Wata kungiyar matasa mai suna kungiyar Ci Gaba ta Mazaje a garin Dambatta Jihar Kano, ta jawo cece-ku-ce sakamakon fassara daban-daban da mutane suke yi mata, sakamakon karar da wata budurwa ’yar kungiyar ta kai ofishin Hisbah na garin.
Wani da ba ya son a bayyana sunansa ya ce ’ya’yan kungiyar matasa ne zalla da ba su wuce shekara 22 da haihuwa ba, kuma duk ’yan makaranta ne wasu ma na firamare.
Ya ce matasan sun kafa kungiyar ce a tsakanin yara maza, inda suke tara kudi suna bayar da gudunmawa ga duk wanda bikin aure ko suna ya faru a gidansu ko danginsu, don shirya liyafa ko kuma dinka kayan anko.
Ya ce daga baya ne yaran suka jawo ’yan matansu cikin kungiyar, suka ci gaba da aiwatar da wannan manufa tasu. “kungiyar ta jima ba a damu da ita ba, sai lokacin da wata ’yar kungiyar mai suna Zainab Idris ta kai kara gaban Hisbah a ranar 23 ga Janairu saboda haushin da ta ji na hana ta wasu kudi da ta tambaya a ba ta taimako.
Bayan da Hisbah ta kira matasan ta ji jawabinsu ne ta kai su gaban Hakimin Dambatta, Alhaji Mukhtari Adnan wanda ya tsawatar musu, tare da mika su ga ’yan sanda don su ja musu kunne.  
Kwamandan Hisbah na garin ya ce ba shi da ikon cewa komai a kan abin, sai dai shugabanninsa.
Haka kokarin jin ta bakin Hakimin da Aminiya ta yi bai yi nasara ba, domin an ce Hakimin ba zai samu fitowa a lokacin da ya je ba. A yayin da wakilinmu ya isa ofishin ’yan sanda inda aka ce yaran suke tsare, bai samu ganinsu ba, kuma an ce masa DPO ba ya nan. Shi kuwa DCO Kabiru Sani ya ce ba ya da masaniya kan lamarin kuma ba ya da ikon yin magana. Mataimakin Daraktan Hisbah na Jihar Kano Barista Nabahani Usman ya ce maganar ba ta zo gabansu ba.