Wata kyanwa

Wani mutum ne matarsa ke da kyanwa, kullum ta dame su da barna. Wata rana sai ya dauke ta, ya yi tafiya mai nisa da ita cikin daji da motarsa. Ya aje motar, ya dauki kyanwar ya yi tafiya mai nisa da ita cikin dajin nan, ya jefar da ita. Ya kama hanyar dawowa sai […]

Wata kyanwa
Wata kyanwa

Wani mutum ne matarsa ke da kyanwa, kullum ta dame su da barna. Wata rana sai ya dauke ta, ya yi tafiya mai nisa da ita cikin daji da motarsa. Ya aje motar, ya dauki kyanwar ya yi tafiya mai nisa da ita cikin dajin nan, ya jefar da ita. Ya kama hanyar dawowa sai ya yi makuwa, ya rasa inda ya aje motar. Tun safe yake tafiya har La’asar bai kai ga inda ya aje motar ba, sai ya buga wa matarsa waya, ya sanar da ita halin da yake ciki. Matarsa ta ce: “Ai kuwa bayan tafiyarka da awa biyu sai ga kyanwar ta dawo gida.” Shi kuwa sai ya kara rudewa, ya ce wa matar: “Ba kyanwar waya mu yi magana da ita”
Daga Lawali Shehu Tsafe 08091573703

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno