Wata mace ta haihu a kasuwa a garin neman mijinta
Wata mace ’yar asalin garin Lafiyan Bare-Bari da ke Jihar Nasarawa mai suna Maryam Sa’idu da take aure a garin Baga, ta haihu a kusa da ’Yan Gwangwan da ke Babbar Kasuwar Gombe lokacin da ta fito neman mijinta mai suna Abba wanda ya bar gida wata biyu da suka wuce lokacin da ’yan Boko […]

Wata mace ’yar asalin garin Lafiyan Bare-Bari da ke Jihar Nasarawa mai suna Maryam Sa’idu da take aure a garin Baga, ta haihu a kusa da ’Yan Gwangwan da ke Babbar Kasuwar Gombe lokacin da ta fito neman mijinta mai suna Abba wanda ya bar gida wata biyu da suka wuce lokacin da ’yan Boko Haram suka tarwatsa garin Baga da ke Jihar Borno.
Maryam mai kimanin shekara 30 ta ce ta Gombe fiye da mako bakwai da suka gabata amma har yanzu ba ta samu labarin inda mijinta yake ba.
Ta ce mijin nata bai gaya mata inda zai je ba “Wannan rikici da ya faru ne ya raba mu tun daga nan ba mu sake haduwa ba har yau, rashin sanin halin da yake ciki ne ya sa hankalina ya tashi na fito yawon nemansa,” inji ta.
Maryam ta ce ta zabi zuwa Gombe ne ko Allah zai sa ta dace saboda ta fi kusa da inda ta baro kuma ba su taba rabuwa na tsawon lokaci haka ba tunda suka yi aure.
Ta c eta je gidan iyayen mijin nata inda suka ce su ma ba su da labarinsa, kuma ba su sani ba ko rikicin ya rutsa da shi ko kuma yana nan da rai ba.
Ta ce da ta je Gombe ta sauka wurin wasu masu sayar da maganin gargajiya tana kwana, daga baya sai ta nemi inda za ta je don ta samu abin yi tana samun abin da za ta ci ita da ’yarta Larai, inda wani
ya tura ta wurin masu surfen shinkafa tana taya su aiki.
Maryam wadda ta ce ta je Gombe da juna biyu, ta ce ta yi fama da yunwa da rashin wurin kwana mai kyau, “Ina wurin tsintar shinkafar ce nakuda ta kama ni na haihu a tsakiyar wani layi ranar Talatar da ta gabata. Bayan na haihu ne jama’a suka taimaka min suka kai ni cikin wani kango na zauna tare da ’yata da jariri,” inji ta.
Maryam ta ce Mai unguwar Herwagana ya sa an taimaka mata da kudi ta kai ’yarta Larai asibiti saboda kamuwa da cutar, amma jaririn da ta haifa yana nan cikin koshin lafiya. “Sai dai kuma ni kaina ina neman taimako domin ko sau daya ban samu na yi wankan ba balle wankan jego,” inji ta.