Wata mai bayar da shawara a kan kisan qare-dangi ta Majalisar Xinkin Duniya Adama Dieng ta ce qasar Burundi na dab da faxawa cikin rikicin da zai iya haifar da aikata manyan laifuka da suka hadar da qashe-qashen mutane. Mista Dieng na wannan jawabi ne ga

Wata mai bayar da shawara a kan kisan kare-dangi ta Majalisar dinkin Duniya Adama Dieng ta ce kasar Burundi na dab da fadawa cikin rikicin da zai iya haifar da aikata manyan laifuka da suka hadar da kashe-kashen mutane.Mista Dieng na wannan jawabi ne ga kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya a lokacin da suke […]

Wata mai bayar da shawara a kan kisan qare-dangi ta Majalisar Xinkin Duniya Adama Dieng ta ce qasar Burundi na dab da faxawa cikin rikicin da zai iya haifar da aikata manyan laifuka da suka hadar da qashe-qashen mutane. Mista Dieng na wannan jawabi ne ga
Wata mai bayar da shawara a kan kisan qare-dangi ta Majalisar Xinkin Duniya Adama Dieng ta ce qasar Burundi na dab da faxawa cikin rikicin da zai iya haifar da aikata manyan laifuka da suka hadar da qashe-qashen mutane. Mista Dieng na wannan jawabi ne ga

Wata mai bayar da shawara a kan kisan kare-dangi ta Majalisar dinkin Duniya Adama Dieng ta ce kasar Burundi na dab da fadawa cikin rikicin da zai iya haifar da aikata manyan laifuka da suka hadar da kashe-kashen mutane.
Mista Dieng na wannan jawabi ne ga kwamitin sulhu na Majalisar dinkin Duniya a lokacin da suke gudanar da wani taro a kan rikicin siyasar kasar, kamar yadda BBC ta bayyana.
Ta ce, “Idan har ba a dauki mataki a kan yadda za a kawo karshen zaman dar-dar din da ake yi a kasar ba, akwai yiwuwar za a sanya wa shugabannin Burundi wadanda ke da hannu a rikicin takunkumi.”
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa ministan harkokin wajen Burundi Alain Aime Nyamitwe ya shaida wa taron kwamitin sulhun cewa yanzu komai ya lafa a kasar, sai dai wasu wurare kadan a Bujumbura.
Hakazalika, Shugaban makwabciyar kasar wato Rwanda, Paul Kagame, ya shawarci Shugaban kasar Burundi game da muhimmancin darussan da yakamata su koya daga kisan kiyashin da ya faru a  shekarar 1994 tsakanin ’yan kabilar Tutsi da kuma Hutu.
Akalla mutune 200 suka rasa rayukansu  yayin dubbai suka kaurace bayan Shugaba Nkurunziza ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takara a karo na uku, inda kuma ya samu nasara a zaben da aka gudanar a watan Yulin da ya wuce.