Wata mai dillacin sassan jikin mutane ta shiga hannu a Ibadan

Wata mata mai suna Saki Adediran da ke dillancin sayar da sassan jikin mutane ga mabukata ta shiga hannun ’yan sanda a Jihar Oyo. Mutane 4 da suke yi wa matar aikin tono sababbin gawarwaki daga cikin kaburbura suna cire sassan jikin da suke bukatata, su ma sun shiga hannu kuma dukkansu ba su musunta […]

Wata mai dillacin sassan jikin mutane ta shiga hannu a Ibadan
Wata mai dillacin sassan jikin mutane ta shiga hannu a Ibadan

Wata mata mai suna Saki Adediran da ke dillancin sayar da sassan jikin mutane ga mabukata ta shiga hannun ’yan sanda a Jihar Oyo.

Mutane 4 da suke yi wa matar aikin tono sababbin gawarwaki daga cikin kaburbura suna cire sassan jikin da suke bukatata, su ma sun shiga hannu kuma dukkansu ba su musunta laifin da ake zarginsu da aikatawa ba.
Da yake nuna wadannan mutane ga ’yan jarida a ofishinsa a Ibadan a Talatar da ta gabata, Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Muhammad Musa Katsina ya ce, “wadannan mutane an dade ana neman su ruwa a jallo, sai yanzu da Allah Ya kawo ni ne asirinsu ya tonu muka kama su cikin tsakar dare a lokacin da suka shiga makabartar Musulmi ta kusa da makarantar Lifefort International da ke Apete a Ibadan, a inda suke tone sababbin kaburbura su yanke sassan jikin gawarwaki kamar hanta da zuciya da koda da kwayar idanu da harshe da kokon kawuna da mazakunta; suna sayarwa ga wannan mata mai suna Saki Adediran da take zuwa daga Legas tana saye daga hannunsu.”
“Bayanan da wadannan mutane su 5 suka yi mana shi ne ya sa muka tura jami’anmu zuwa Legas da suka kama wannan mata da ke hada-hadar sayar da sassan jikin mutane ga wasu manyan mutane. Tuni na aika da yarana domin su yi binciken kwakwaf da zai ba su damar gano mutanen da suke sayen sassan jikin dan Adam domin a kamo su a gurfanar da su gaban kotu.”
Haka kuma kwamishinan ya nuna wa ’yan jarida wani Bafulatani matashi mai suna Isah Buruku da yake yin amfani da motarsa wajen daukar kyawawan mata a kan hanya da yake ba su kyautar lemon kwalba mai dauke da sinadarin barci. Da zarar sun sha wannan lemo sai hankalinsu ya gushe daga jikinsu ya shiga cikin daji ya yi musu fyade tare da kwashe dukkan abun da yake tare da su har da suturun da suke sanye ya bar su tsirara.
Duka-duka kimanin mutane 30 maza da mata ne rundunar ’yan sandan ta kama da fashi da makami da satar kananan motoci masu tsada guda 23 da babura da wayoyin kamfanonin sadarwa da barayin suka sace daga hannun wadanda suka mallake su a jihohin Legas da Ogun da Oyo da Kwara da bindigogi da harsasai da sauran makamai da layu da guraye da kuma wasu mutane 2 masu suna Bala Aliyu da Yahaya Muhammad da suke zaune a Kano a matsayin masu karbar motocin sata daga hannun barayin da suke kai musu.
Wani abun da ba a saba gani ba shi ne, yadda Kwamishinan ’yan sandan ya mika makullan wata karamar mota ga direbanta mai suna Jami’u Adebayo a nan take bayan ’yan sanda sun kwato motar daga hannun barayin da suka sace ta. “Babu wani dalilin ci gaba da ajiye motar na tsawon lokaci tun da mun kammala bincike kuma mun tabbatar motar mallakar wannan mutumi ce,” inji shi.