Wata mai fataucin yara ta shiga komar ’yan sanda a Jigawa
Dubun wata mata ’yar shekara 60 da haihuwa ya cika, inda ’yan sanda suka kama ta dauke da kananan yara masu karancin shekaru daga matakin shekara 9 zuwa 13 da haifuwa, tana kokarin kai su Kaduna domin yin aikatau a gidajan mutane. Matar mai suna Ladi dahiru, ’yar asalin kauyan Sada ce da ke cikin […]
Dubun wata mata ’yar shekara 60 da haihuwa ya cika, inda ’yan sanda suka kama ta dauke da kananan yara masu karancin shekaru daga matakin shekara 9 zuwa 13 da haifuwa, tana kokarin kai su Kaduna domin yin aikatau a gidajan mutane.
Matar mai suna Ladi dahiru, ’yar asalin kauyan Sada ce da ke cikin karamar Hukumar ’Yankwashi, Jihar Jigawa, an kama ta ne a kan hanyarta ta zuwa Kaduna, Unguwar Kabalan Doki.
’Yan sanda masu sintiri ne suka kama ta, ta ce makarantar Islamiyya za ta kai yaran Kaduna, alhali kamar yadda bincike ya nuna matar ba ta da wajen da za ta sauki yaran, domin dakinta daya ne ciki da falo kuma ba ta da wata sana’a ta kirki.
Yanzu dai haka matar tana hannun ’yan sanda, a garin Dutse, suna gabatar da bincike a kanta kuma da zarar an kammala za su mika ta ga hukumomin da ya dace, domin daukar matakin shari’a.
Jami’in hulda da jama a na rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa, DSP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar labarin. Ya ce ya kara da cewa yaran kanana ne kuma suna zargin matar da cewa ta debo su ne da nufin ta sanya aikin wahala a gidajan mawadata, tana amsar kudi, sabanin yadda ta yi wa iyayensu karyar cewa za ta sanya su a makarantar Islamiyya.
Kamar yadda binciken ’yan sanda ya nuna, matar ta debo yaran ne daga hannun iyayensu, daga wani kauye mai suna Falle, da ke cikin karamar Hukumar kunci, a Jihar Kano. Kuma ta kwaso su ne daga gidaje daban-daban daga kauyan, da nufin za ta taimaka masu.
Daga cikin wadanda aka samu matar da su akwai Hassana Abdullahi, Basira Isa, Rukayya Idi, Halima Sadiya Bala da Habiba Musa da Zainab danyaro da Halima Lawal da A’isha Muhammad da kuma Wasila Yahaya.
’Yan sanda a jihar sun gargadi iyaye da su guji bai wa miyagun mutane ’ya’yansu suna amfani da su wajen sanya su ayyukan bauta, inda ake azabtar da su a gidajan aikatau.