wata makarantar ma ta kama da wuta

A ranar Larabar da ta gabata kuma wata gobarar ta sake kamawa a makaranatar maza ta gwamnati da ke Kwankwaso, yankin karamar Hukumar Madobi cikin Jihar Kano. Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 7:45 na safe, inda ta cinye wasu daga cikin dakunan kwanan daliban kurmus. Sai dai ba a […]

wata makarantar ma ta kama da wuta
wata makarantar ma ta kama da wuta

A ranar Larabar da ta gabata kuma wata gobarar ta sake kamawa a makaranatar maza ta gwamnati da ke Kwankwaso, yankin karamar Hukumar Madobi cikin Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 7:45 na safe, inda ta cinye wasu daga cikin dakunan kwanan daliban kurmus. Sai dai ba a rasa rai a lokacin tashin gobarar ba. Haka kuma babu wanda ya sami rauni.
Jami’in Hulda da Jama’a na ofishin Mataimakin Gwaman Kano wanda kuma shi ne Kwamishinan Ilimi na jihar, Farfesa Hafiz Abubakar, Malam Usman Bello ya bayyana cewa kasancewar gobarar ba ta shafi ajujuwan daliban ba, ya sa gwamnati ta bayar da umarnin a ci gaba da karatu a makarantar ba tare da an rufe ta ba.