Wata malamar sakandare a Abiya ta hadu da fushin iyayen yarinya

A Jihar Abiya, wasu iyalai sun lakada wa wata malamar makarantar Sakandaren Ozar duka. Malamar da ke yankin Asa, karamar Hukumar Ukwa ta yamma ta gamu da matsalar ce, sakamakon umartar wata daliba mai suna Precious Nwadike cewa ta je ta yi saisayen gashin kanta, lamarin da bai yi wa yarinyar da iyayenta dadi ba. […]

Wata malamar sakandare a Abiya ta hadu da fushin iyayen yarinya
Wata malamar sakandare a Abiya ta hadu da fushin iyayen yarinya

A Jihar Abiya, wasu iyalai sun lakada wa wata malamar makarantar Sakandaren Ozar duka.

Malamar da ke yankin Asa, karamar Hukumar Ukwa ta yamma ta gamu da matsalar ce, sakamakon umartar wata daliba mai suna Precious Nwadike cewa ta je ta yi saisayen gashin kanta, lamarin da bai yi wa yarinyar da iyayenta dadi ba. Wannan dalili ya sa suka yanke shawara kuma suka yi tafiyayya har makarantar suka doki malamar.
Malamar mai suna Misis Njoku, ta ce ta umarci dalibar ce da yin haka, domin haka ka’idar makarantar ta shimfida. “Daga nan ne fa sai suka yi gayyar mamarta da kanne da yayyenta, suka zo nan makaranta kamar abun arziki; suka kira ni sai zage-zage sai duka. Na ji kurum sun rufe ni da duka.” Inji ta.
Haka kuma Aminiya ta kalato cewa, tun kwanan baya ma ashe m++++alaman makarantar sun gargadi dalibar tasu da ta je ta yi saisayen gashin kanta, amma ta kiya. Ganin haka sai ranar Litinin da dalibai suka zo makaranta ne aka umarci duk wadda ba ta yi saisayen gashin kanta ba da ta je gida maza yanzu ta yi.
Ganin yadda al’amarin bai yi wa makaranta da malamanta dadi ba, shugabar makarantar uwargida F. N. Nwachukwu ta tabbatar da kama uwar dalibar mai suna Misis Nwadike da wani daga cikin ’ya’yanta mai suna Uche. Ita kuma malamar da aka lakada wa duka, wani malami mai suna Izuchukwu Nwakoama ne ya garzaya da ita asibiti, yaran kuma aka kai su ofishin ’yan sanda na Obehie.