Wata mata a Ingila ta zargi ’yar tsana da furta miyagun kalamai
Wata mata a Ingila ta zargi ’yar tsanar ’yarta da furta kalmomin batanci, don haka ta yi tir da ita, kamar yadda shafin sadarwa na UPI.com ya ruwaito.Talina Woods, ’yar shekara 25, wadda ta fito daga yankin wales, ta sayi diyar bebi, “mai Magana ‘talking Barbiee Doll,” wadda ta saya wa ’yarta Demileigh, ana kuma […]
Wata mata a Ingila ta zargi ’yar tsanar ’yarta da furta kalmomin batanci, don haka ta yi tir da ita, kamar yadda shafin sadarwa na UPI.com ya ruwaito.
Talina Woods, ’yar shekara 25, wadda ta fito daga yankin wales, ta sayi diyar bebi, “mai Magana ‘talking Barbiee Doll,” wadda ta saya wa ’yarta Demileigh, ana kuma sa ran za ta rika furta kalmomin farin ciki da jin dadi, wadanda suka hada da “zuwa gidan gyaran gashi – to the salon,” ko “ina kaunar kayan kwalliya – I lobe a makeober.”\
Demileigh ta yi wasa da ’yar bebintan na tsawon kwana biyu, kafin mahaifiyarta ta ji cewa ’yar tsanar ta furta miyagun kalmomi, wadanda suka fara da haruffan W da T da F.
Sai dai wadanda suka ji kalaman ’yar tsanar, sun ce tana furta cewa, “Off the hook,” daya daga cikin kalaman da take furtawa kafin a yi mata saiti. Duk da haka Woods ta ce, ba za ta yi sakwa-sakwa ba. Don haka sai ta fitar diyar bebi mai furta miyagun kalamai daga wajen ’yarta Demeleigh.
A da Woods ta yi nufin mayar da wnanan diyar bebi zuwa kantin da ta sawo ta, amma sai ta tuna dole sia da rasiti, kamar yadda jaridar HuffPost ta Birtaniya ta ruwaito.