Wata mata mara fasfo ta hau jirgi daga Amurka zuwa Birtaniya babu tikiti

Wata mata Marilyn Hartman, mara galihu da ba tama dagidan kwana  ta shammaci jami’an tsaro ta hau jirgin saman British Airways, inda tatashi da Amurka zuwa  Landan a kasar Birtaniya ba tare da tikiko fasfo ba. Marilyn Hartman ta saje da dimbin jama’a ne a filin jirgin saman Chcago na O’Hare, inda ta hau jirgin […]

Wata mata mara fasfo ta hau jirgi daga Amurka zuwa Birtaniya babu tikiti
Wata mata mara fasfo ta hau jirgi daga Amurka zuwa Birtaniya babu tikiti

Wata mata Marilyn Hartman, mara galihu da ba tama dagidan kwana  ta shammaci jami’an tsaro ta hau jirgin saman British Airways, inda tatashi da Amurka zuwa  Landan a kasar Birtaniya ba tare da tikiko fasfo ba.

Marilyn Hartman ta saje da dimbin jama’a ne a filin jirgin saman Chcago na O’Hare, inda ta hau jirgin har ta sauka a babban filin saukar jiragen saman Heathrow da ke Landan a kasar Birtaniya.

Masu kula da walwalar fasinjoji sun gano cewa matar ba ta da tikiti, don haka aka kamat aa filin jirgin saman Heathrow da ke Landan, inda akamayar da ita Chicago a kasar Amurka. Hartman mai shekarar 66 ta gurfana a gaban kotu, inda aka tuhumeta da laifin sata da keta haddin doka, sannan ’yan sanda sun ce ta shafe sa’a 24 a filin jirgin saman Chicago kafin ta hau jirgi, amma ma’aikatan filin jirgin saman sun dauka kawai a rude take, a cewar rahoton jaridar The Mirror.

Sai dai an ce ba wannan nekaron farko da aka taba kama Hartman tana yunkurin kutsa kai cikin filin jirgin sama har ta shamamci jami’an tsaro a Amurka, sun ma yi ikrarin cewa ta sha hawan jiragen sama ba tare da tikiti ba, har sau takwas. Ta bayyana wa ’yan sanda cewa ta fi samun natsuwa in tana zaunree a filin jirgin fiye da ta yi ta gararamba a kan tituna.

Shekara uku da ta gabata an taba kama Hartman tana sandon hawa jirgin sama, sa’o’ikadan bayan ta fito daga kurkuku. Sannan a shekarar 2016 ankaita gidan masu tabin hankali, inda ta yi zaman shekara biyu.

Jami’an tsaron harkokin sufuri sun dukufa wajen gudanar da bincike kan lamarin, kamar yadda rahoton ya bayyana. “Jami’an tsaron na TSA da takwarorinsu na hukumar sufurin jiragen sama sun dauki matakan gaugawa wajen sake nazarin yadda sza ainganta harkokin tsaro a daukacin filin jirgin saman,” kamar yadda yake kunshe a rahoton.